Kabilu Biyar Na Tsaunin Mambila Sun Yi Taron Hana Barkewar Rikici Tsakaninsu

A karkashin wata kungiyar wanzar da zaman lafiya, wasu kabilu biyar daga tsaunin Mambila sun yi taro a garin Gembu domin kawo zaman lafiya a yankin

Kabilu Biyar Na Tsaunin Mambila Sun Yi Taron Hana Barkewar Rikici Tsakaninsu

Kabilun tsaunin Mambila biyar ne suka taru a filin wasan garin Gembu domin rigakafin hana sake barkewar duk wani rikici da sunan kabilanci ko addini ko kiyayyar manoma da makiyaya. An gudanar da taron ne a karkashin wata kungiya mai wanzar da zaman lafiya. Shugaban kwamitin karamar hukumar, Pastor Godwin Sawa ya ce fitinar da […]

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun koka a kan hali da mutanen Mambila ke ciki

Hadakar kungiyoyin kare hakkin bil Adama ta koka game da halin ko in kula da shugabanin ke nunawa akan halin da yan gudun hijira na yankin Mambila a jihar Taraba suke ciki, musamman ta fuskar kiwon lafiya.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun koka a kan hali da mutanen Mambila ke ciki

Kungiyoyin sun ce yan gudun hijiran musamman wadanda suka ketara zuwa kasar Kamaru na bukatar agaji, musamman daga gwamnatin jihar. Hadakar kungiyoyin kare hakkin bani adaman da kuma yan fafutuka da suka hada da Centre For Human and People’s Right Advocacy da Taraba Concern Citizens Forum, sun koka ne a lokacin da suka kai ziyarar […]

Za a Kai Gwamnatin Taraba kotun ICC

Za a Kai Gwamnatin Taraba kotun ICC

  Wani babban Laura Farfesa Yusuf Dankofa tare da kungiyar Miyatti Allah sun bayyana cewar za su maka Gwamnatin Taraba a kotun hukunta laifukan yaki ta duniya bisa zargin hannu a kisan kiyashi da aka yi wa fulani a Mambila dake jihar. A wata hira da yayi da sashen Hausa BBC, Farfesa Yusuf Dankofa yace […]

Tawagar Sanata Musa Kwankwaso Ta Kai Ziyara Tsaunin Mambila

Rashin ayyukan yi, ilimi da shaye shaye tsakanin matasa na daga cikin dalilai da suke haddasa tashe tashen hankula da suka abku a yankin tsaunin Mambila na karamar hukumar Sardsauna dake jihar Taraba.

Tawagar Sanata Musa Kwankwaso Ta Kai Ziyara Tsaunin Mambila

Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar tarayya ta Kano ta tsakiya a Sanata Musa Kwankwaso yana mai cewa matasan da basu da aikin yi ne ake anfani dasu wajen haddasa tashe tashen hankali. Ya furta haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar mazabarsa ziyarar jajantawa da ban hakuri ga mazauna yankin da ke da Hausawa […]