Dalilin Da Ya Sa Muka Ce a Cafke Shugabannin Kungiyoyin Matasan Arewa – Gwamnati

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana dalilin da ya sa ta nemi izinin kama shugabannin kungiyoyin matasan arewa wadanda suka ba kabilar Igbo wa'adin wata uku su bar duk jihohin arewacin kasar.

Dalilin Da Ya Sa Muka Ce a Cafke Shugabannin Kungiyoyin Matasan Arewa – Gwamnati

Gwamnatin jihar Kaduna tace dalilin samun izinin kama shugabannin kungiyoyin matasan arewan Najeriya da suka baiwa ‘yan kabilar Igbo wa’adi su bar arewacin kasar shi ne tabbatar da an bi doka da oda duk da janye wa’adin da suka yi. Da yake karin haske gameda sanarwar da gwamnatin ta fitar akan kamo shugabannin, mai magana […]

Ni Yakamata Ku Farwa, Ba ‘Yan Kabilar Igbo Ba, Sako Daga Sarkin Musulmi Zuwa Samarin Arewa

Ni Yakamata Ku Farwa, Ba ‘Yan Kabilar Igbo Ba, Sako Daga Sarkin Musulmi Zuwa Samarin Arewa

Daga Sokoto- Maigirma Sarkin Musulmi Sultan Abubakar ya ce duk wanda yake da shirin kaiwa ‘yan kabilar Igbo mazauna arewacin kasar hari, to shi yakamata ya fara kaiwa wannan harin. Sarkin musulmin ya fadi haka ne lokacin da shugaban kabilar Igbon ta duniya, Dr Mishack Nnanta tare da rakiyar shugabannin kabilar Igbo mazuna yankin suka […]

Al’umman Igbo Sun Yi Na’am da Janye Shirin Korarsu daga Arewacin Najeriya

A watan Mayu ne gamayyar kungiyoyin matasan arewa suka ba 'yan kabilar Igbo dake zaune jihohin arewa har zuwa daya ga watan Oktoba su koma yankinsu, yankin da Nnamdi Kanu yake neman ya balleshi daga tarayyar Najeriya ya kafa kasar Biafra

Al’umman Igbo Sun Yi Na’am da Janye Shirin Korarsu daga Arewacin Najeriya

‘Yan kabilar Igbo dake arewacin Najeriya sun yi na’am da matakin da gamayyar kungiyoyin matasan arewa suka dauka na janye shirin korarsu daga jihohin arewa kafin daya ga watan Oktoba na wannan shekarar. Da dama daga cikin mutanen Igbo suka yanke shawarar cigaba da zamansu a arewa kafin janyewar. Amma sun ce matakin ya faranta […]

Kungiyar Tuntubar Juna Ta Dattijan Arewa (ACF) Tayi Maraba Da Janye Ummarnin Da Aka Bawa ‘Yan Kabilar Igbo Na Ficewa Daga Yankin

Kungiyar Tuntubar Juna Ta Dattijan Arewa (ACF) Tayi Maraba Da Janye Ummarnin Da Aka Bawa ‘Yan Kabilar Igbo Na Ficewa Daga Yankin

Kungiyar Tuntubar Juna ta Dattijan Arewa tayi maraba da matakin da Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa suka dauka na janye ummarnin da suka bawa  ‘yan kabilar Igbo mazauna arewa ficewa daga yankin ranar 1 ga watan Oktoba. Inda kungiyar ke cewa “Wannan wani cigaba ne mai kyau da zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da cigaban […]

Kungiyar ACF ta bayyana cewar matasan arewa sun yi abin da ya dace

Kungiyar ACF ta bayyana cewar matasan arewa sun yi abin da ya dace

Kungiyar tuntuba ta dattawan arewacin Najeriyar, ta ce tun da matasan suka bayar da wa’adi na cewa al’ummar Igbo su tattara na su ya na su su koma yankunansu kafin 1 ga watan Oktoba mai zuwa, su ke ta tattaunawa da su domin samun maslaha. A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai […]

Babu inda ‘yan kabilar Igbo zasuje – Ganduje

Babu inda ‘yan kabilar Igbo zasuje – Ganduje

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana cewa babu inda ‘yan kabilar Igbo mazauna birnin na Kano zasuje a sakamakon wa’adi da kungiyar matasan Arewa ta basu. Gamna Ganduje ya bayyana hakan ne a jiya Asabar 5 ga watan Augusta a yayin wata ziyara da ‘yan kungiyar Ibgo suka kai masa inda yake […]

Matasan Arewa Sun Nufi Majalisar Dinkin Duniya Akan Biafra

Matasan Arewa Sun Nufi Majalisar Dinkin Duniya Akan Biafra

WASHINGTON DC — Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa a Karkashin jagorancin Ambasada Shettima Yarima wadanda suka ba Kabilar Igbo wa’adin watanni uku sun aikewa Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guetarres da takarda mai shafuka 20 inda suka nemi Majalisar Dinkin Duniya ta shiga batun baiwa yankin Biafra cin gashin kanta da ke neman kawo wa Najeriya matsala. […]