Yadda Tsananin Kadaici Ke Juya Kwakwalwa

Kwakwalwar Sarad Shourd ta fara juyewa bayan an tsareta a kurkuku tsawon wata biyu. Ta rika jin takun sawun fatalwa da walkiya na haskawa, inda a mafi yawan kwanaki take shafe yini a sunkuye tana saurare ta kafar kofa.

Yadda Tsananin Kadaici Ke Juya Kwakwalwa

A wannan yanayin zafin, wannan mata ‘yar shekara 32 ta yi hawan tsauni tare da kawayenta a tsaunukan Kurdistan da ke kasar Iraki, a daidai lokacin da sojojin Iran suka kama su, bayan da suka kauce suka tsallaka kan iyaka zuwa cikin Iran. An zarge su da leken asiri, inda aka tsare su a wani […]