Saudiya Da Iran Za Su Kai Wa Juna Ziyarar Diflomasiya

Iran ta ce nan gaba kadan jami’an diflomasiyar kasashen biyu za su ziyarci Saudiya domin fahimtar juna a wani yunkuri na dinke sabani da barakar da ke tsakaninsu bayan sun yanke hulda a bara.

Saudiya Da Iran Za Su Kai Wa Juna Ziyarar Diflomasiya

Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi ga daliban kasar, inda ya ce za a yi ziyarar ne bayan kammala aikin Hajjin bana. Zarif ya ce tuni aka ba jami’an da za su gudanar da ziyarar iznin shiga kasashen, abin da suke jira kawai shi ne mataki […]