An Kama Wadanda Suka Yi Wa Wata Mata Fyade a Mota

An kama wasu mutum hudu a birnin Casablanca, bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna yadda aka ci zarafin wata mata ta hanyar yi mata fyade a motar bas.

An Kama Wadanda Suka Yi Wa Wata Mata Fyade a Mota

Faifan bidiyon, wanda ya bayyana a ranar Lahadi, ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a shafukan sa da zumunta. Ya nuna yadda matasan ke dariya yayin da suke cin zarafin matar. Kamfanin sufuri na M’Dina Bus ya fitar a wata sanarwa cewa, an kama wadanda suka aikata laifin a ranar Litinin. Ya kara da cewa, ana bincike […]