‘Yan majalisar Nigeria sun sayi motocin ‘kece-raini’ 200

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun saya wa kansu motoci na alfarma 200 kirar fijo 508 daga kamfanin kera fijo na kasar, Peugeot Automobile Nigeria Limited.

‘Yan majalisar Nigeria sun sayi motocin ‘kece-raini’ 200

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Mr. Abdulrazak Namdas, ya shaida wa BBC cewa an sayi motocin ne domin ‘yan majalisar su samu damar gudanar da ayyukan kwamitoci da kyau. Wannan lamari dai na zuwa ne a lokacin da ‘yan kasar da dama suke kokawa kan tsananin talauci da tsadar kayayyaki da ake fama da […]