Sunan Muhammad Ya Samu Matsayi A Birtaniya

Wani rahoto da hukumar kididdiga ta Birtaniya ta fitar ya nuna cewa sunan Muhammad ya samu gagarumar karbuwa a Ingila, inda ya kasance cikin sunaye 10 da iyaye suka fi sanya wa 'ya'yansu a yanzu.

Sunan Muhammad Ya Samu Matsayi A Birtaniya

Sunan na Muhammad wanda kafin wannan lokaci ba ya cikin goman farko da suka fi farin jini, a yanzu ya kawar da sunan William ya hau gurbi na goma a jerin sunayen da aka fi rada wa yara. A alkaluman da hukumar ta fitar ta ce sunan Oliver wanda shi ne na daya cikin sunayen […]