Ya Kamata Buhari Ya Duba Kalaman Matarsa — Okorocha

Gwamnan jihar Imo a Najeriya, Rochas Okorocha, ya bi sahun matar shugaban kasar, Aisha Buhari wadda ta yi korafin cewa mijinta ya yi watsi da 'yan jam'iyyarsa ta APC a harkokin mulki.

Ya Kamata Buhari Ya Duba Kalaman Matarsa — Okorocha

Rochas Okorocha ya ce ya kamata shugaba Buhari ya saurari korafin matar tasa musamman wajen yi wa mukarraban gwamnatinsa garanbawul. Okorocha wanda ya bayyana hakan a karshen mako, ga ‘yan jaridu, a fadar gwamnati, ya ce, “tabbas ni gwamna ne kuma na san inda gizo yake sakar.” Ya kara da cewa “idan dai har akwai […]