An kori ‘yan sandan da ‘suka wawushe gidan Jonathan’

Rundunar 'yan sandan babban birnin Najeriya, Abuja, ta kori 'yan sanda hudu da ake zargi da hannu a wawushe wani gidan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, da ke unguwar Gwarimpa a Abuja.

An kori ‘yan sandan da ‘suka wawushe gidan Jonathan’

Wata sanarwar da rundunar ta fitar ta ce bayan an gudanar da bincike kuma an samu ‘yan sandan da ke gadin gidan tsohon shugaban kasan da hannu cikin satar da aka yi a gidan, kwamishinan ‘yan sandan birnin, CP Musa Kimo, ya amince da korar ‘yan sandan hudu. Wadanda aka kora din sun hada da […]