Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

A Najeriya sojojin kasar da dama na jibge a wasu yankuna domin gudanar da sintiri da atisaye, musamman domin kwantar da hankulan jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya. Shin mene ne tasirin irin wannan sintiri?

Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

 A sassa daban daban na Najeriya dakarun kasar kan gudanar da atisaye na musamman inda akan jibge su su yi kwana da kwanaki ko kuma su dauki wani tsawon lokaci suna atisayen. Akan kai dakarun ne yankunan da ke fama da wasu matsaloli na musamman, misali a yankin da ake fama da matsalar satar shanu […]

Taron kayan sawa da na kwalliyar da aka sarrafa a Afrika

An fara taron baje kolin kayakin sawa dana kwalliyar da aka sarrafa a Nahiyar Africa a Abuja babban birnin Najeriya da nufin bunkasa harkar tare da dakile amfani dana kasashen Turai.

Taron kayan sawa da na kwalliyar da aka sarrafa a Afrika

An dauki tsawon lokaci Al’ummar nahiyar Afrika na amfani da kayakin da aka sarrafa a kasashen Turai musamman a bangaren daya shafi kayakin kwalliya da na sawa, sai dai da alamu hankalin ‘yan Afrikan ya fara karkata zuwa amfani da kayakin da aka sarrafa a Gida. Hakan dai na da nasaba da taron da yanzu […]

NLC ta nesanta kanta daga ikirarin durkusar da harkoki a Najeriya

Kungiyoyin kwadagon Najeriya, sun nesanta kan su daga ikrarin wata kungiya ta UCL, da ta yi ikirarin cewa a yau 18 ga Satumba zata durkusar da kasar saboda rashin yi mata rajista.

NLC ta nesanta kanta daga ikirarin durkusar da harkoki a Najeriya

Kungiyoyin kwadagon Najeriya, sun nesanta kan su daga ikrarin wata kungiya ta UCL, da ta yi ikirarin cewa a yau 18 ga Satumba zata durkusar da kasar saboda rashin yi mata rajista. A makon daya gabata ne, kungiyar ta UCL, ta bukaci ma’aikata su tsunduma cikin yajin aiki, su kuma rufe tashoshin jiragen sama da […]

Ana Duba Hanyar Magance Cin Zarafin Kananan Yara A Nigeria.

Masana harkokin shara'a suna gudanar da taro a jihar Adamawa da niyyar lalubo hanyar da za a kawo karshen cin zarafin yara da mata. Mahalarta taron dai sun kunshi kwamishinonin shara'a ne na daukacin jihohin tarayyar Nigeria, kuma MInistan Shara'a Abubakar Malami ne ya bude taron

Ana Duba Hanyar Magance Cin Zarafin Kananan Yara A Nigeria.

Hukumomin shara’a a Nigeria sun gudanar da wani taro domin samo hanyar magance cin zarafin yara kanana da mata. Dukkan Kwamishinonin sharia ne na daukacin dukkan jihohin Nigeria ne ke halartan wannan taron. Da yake wa manema labarai karin haske, Ministan shariar Najeriya Abubakar Malami yace an shirya taron ne don duba rawar da hukumomin […]

Olympics: Za’a Mikawa ‘Yar Najeriya Lambar Tagulla Bayan Shekaru 9

Maryam Usman, wadda ta wakilci Najeriya a gasar daga nauyi na kilogram 75 ajin mata, a wasannin Olympics da ya gudana a Beijing, shekara ta 2008

Olympics: Za’a Mikawa ‘Yar Najeriya Lambar Tagulla Bayan Shekaru 9

Kwamitin lura wasannin Olympics na Najeriya y ace a ranar Alhamis dinnan mai zuwa zai mika kyautar lambar yabo ta tagulla ga Maryam Usman, wadda ta wakilci kasar a gasar daga nauyi na kilogram 75 ajin mata, a wasannin Olympics da ya gudana a Beijing, shekara ta 2008. Maryam zata amshe kyautar tagullan ce, sakamakon […]

Shin ko har yanzu ana amfani da biro wajen rubutu?

Tun bayan bullar sabbin hanyoyin rubutu kamar Komfuta da wayoyin salula, kasuwar alkalami ko kuma biro ta ja baya

Shin ko har yanzu ana amfani da biro wajen rubutu?

A halin da ake ciki a yanzu, ko da sako ne mutum zai rubuta, to da sabbin hanyoyin rubutun na zamani ake amfani. A Najeriya ma dai haka abin ya ke, domin da yawa daga cikin al’ummar kasar musamman matasa da manya ma’aikata, su kan jima ba su yi rubutu da biro ba, saboda sun […]

EFCC Ta Gano Naira Milyan 300 Cikin Wata 4 A Shiyyar Oyo.

Mataimakin shugaban hukumar a shiyyar kazeem Hussein ne ya bayyan ahaka a wani taron manema labarai.

EFCC Ta Gano Naira Milyan 300 Cikin Wata 4 A Shiyyar Oyo.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, shiyyar jahar Oyo ta gano Naira milyan 300 cikin watanni hudu da suka gabata. Mataimakin shugaban hukumar reshen jahar Oyo Kazim Hussein, shine ya bayyan haka lokacinda yake magana da manema labarai kan ayyukan hukumar a yankin. Mr. Kazeem yace cikin wadanda hukumar ta […]

Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasahen ketare jinya?

Shugabannin kasashen Najeriya da Angola da Zimbabwe da Benin, da Algeria na da abubuwan da suke kamanceceniya, wato rashin yarda da tsarin kiwon lafiyar kasashensu.

Me ya sa shugabannin Afirka ke zuwa kasahen ketare jinya?

Ta fuskar lokutan da suka shafe suna jinya a kasar waje, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 74, shi ne na farko a cikinsu, amma a shekarun da suka gabata dukkan wadannan shugabannin sun ketara wasu kasashen don duba lafiyarsu. A lokuta da dama suna tafiya su bar asibitoci ba isasshen kudin da za […]

Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan ‘yan gudun hijira

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soki majalisar dinkin duniya da sauran kungiyoyin bayar da agaji saboda "zuzuta" halin da 'yan gudun hijirar da Boko Hara suka kora daga gidajensu ke ciki.

Buhari ya soki majalisar dinkin duniya kan ‘yan gudun hijira

A wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce kungiyoyin suna kambama halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki ne da zummar samun kudi daga wajen gwamnatoci. Ya bayar da sanarwar ce kwanaki kadan bayan majalisar ta dinkin duniya ta ce fiye da mutum 5m da Boko Haram ta raba […]

Sojin Nigeria ‘sun kai samame’ ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce dakarun tsaron Nijeriya sun kai samame kan daya daga cikin ofisoshinta a yankin arewa maso gabashin kasar, inda suka gudanar da bincike ba tare da izini ba.

Sojin Nigeria ‘sun kai samame’ ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya

Wata mai magana da yawun Majalisar ta fada wa BBC cewa binciken, wanda aka shafe tsawon sa’a uku ana yi, an kaddamar da shi ne da sanyin safiyar ranar Juma’a a birnin Maiduguri. Majalisar Ɗinkin Duniya na da yawan jami’ai a arewa maso gabashin Najeriya, inda suke bayar da tallafi ga mutanen da rikicin Boko […]

1 2 3