‘Ko Buhari Ya Tambaye Su Aikin Yi Nawa Aka Samar?’

Wasu masana tattalin arziki a Nijeriya, sun fara kalubalantar shugaban kasar Muhammadu Buhari game da farin cikin da ya nuna kan bayanin farfadowar tattalin arzikin da ministocinsa suka ce ya yi.

‘Ko Buhari Ya Tambaye Su Aikin Yi Nawa Aka Samar?’

Dr. Nazifi Darma ya ce kamata ya yi shugaban ya tambayi ministocinsa ko mutum nawa aka samarwa ayyukan yi sakamakon ci gaban da suke ikirarin (tattalin arzikin) kasar ta samu. “Ayyuka miliyan nawa aka samar?” “Kuma game masana’antun da suka durkushe, guda nawa ne suka bude suka ci gaba (da aiki). Kuma me suka sarrafa?”, […]