An Yi Gangamin Ilimantar da Jama’a Kan Illar Ambaliyan Ruwa

Yau a Kano hukumar kula da harkokin ruwa ta najeriya ta gudanar da taron ganganmin wayar da kan jama’a dangane da hanyoyin kaucewa annobar ambaliyar ruwa.

An Yi Gangamin Ilimantar da Jama’a Kan Illar Ambaliyan Ruwa

Hukumar kula da harkokin ruwa da yanayi ta Najeriya ta gudanar da taron yawar da kawunan jama’a akan illar ambaliyan ruwa Taron ya kunshi masu ruwa da tsaki da suka hada da masana kan lamuran albarkatun ruwa da raya gandun daji, da kwararraru kan harkokin muhalli da sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati kan sha’anin tsara […]

Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

A ranar Laraba ne kwale-kwale ɗauke da 'yan kasuwa 150 daga kauyen Gaya cikin jamhuriyar Nijar da ke kan hanyar zuwa kasuwa a garin Lolo a jihar Kebbi ya kife.

Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

An samu ceto mutane 50 daga cikinsu. Har yanzu ma’aitakan ceto daga jamhuriyyar Nijar da Najeriya na ci gaba da aikin ceton waɗanda suka rage. Sai dai babu tabbas cewa za’a same su a raye. A halin yanzu an kai wadanda aka ceto asibitin Lolo domin samun magunguna da kulawa. Jami’an hukumar bada agajin gaggawa […]

Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Ana samun alkaluma masu cin karo da juna na adadin mutanen da suka rasu sakamakon gobara a wata masana'antar iskar gas a garin Nnewi na jihar Anambra.

Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Hukumomin ‘yan sanda wadanda suka tabbatar da aukuwar gobarar, ba su yi karin haske ba dangane da adadin mutanen da suka kone ba. Hukumar agaji ta NEMA ta ce mutane biyar ne suka rasu a yayin da mutane bakwai suka samu raunuka. NEMA ta ce gidaje shida da motoci 22 ne suka kone sakamakon gobarar. […]

Mutane 15 ne ambaliyar ruwa ta kashe a Suleja

'Ita ce ambaliyar ruwa mafi muni da muka samu a Suleja'

Mutane 15 ne ambaliyar ruwa ta kashe a Suleja

Akalla mutum 15 ne suka mutu bayan saukar wani ruwan sama a unguwar Kaduna-Road kusa da Abuja a Najeriya, kamar yadda wani ganau ya shaidawa BBC. Alhassan Danbaba ya ce gadoji da gidaje fiye da talatin ne ambaliyar ruwan ta yi gaba da su, na yankin karamar hukumar Suleja mai makwabtaka da birnin Abuja. Ya […]