Venezuela ta daura damarar kare iyakokinta

Venezuela ta daura damarar kare iyakokinta

Gwamnatin Venezuela ta ce dakarunta dubu 200 da kuma fararen hula dubu 700 sun bi sahun atisayen soji na ranar farko da aka yi. An shirya atisayin ne bayan Amurka ta sanar da sanya takunkumin tattalin arziki a kan gwamnatin shugaba Maduro. Amurka dai na zargin Mr Maduro da yin mulkin kama karya. Shugaba Maduro […]

Amurka ta saka wa jami’an Venezuela 13 takunkumi

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya yi fatali da takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wasu manyan 'yan siyasa da jami'an sojin kasarsa goma sha uku.

Amurka ta saka wa jami’an Venezuela 13 takunkumi

Amurka dai ta ce ta dauki matakin domin nuna wa Mr. Maduro cewa da gaske take a barazanar ta yi na kakaba wa Venezuela takunkumi karya tattalin arziki cikin sauri idan ya ci gaba da shirinsa na gudanar da wata kuri’ar da aka shirya yi ranar Lahadi mai zuwa domin kafa wata sabuwar majalisar dokoki. […]

An lakadawa ‘yan majalisar Venezuela duka

An lakadawa ‘yan majalisar Venezuela duka

Masu goyon bayan gwamnatin Venezuela sun kutsa kai cikin majalisar dokokin kasar inda suka yi wa ‘yan majalisar da ‘yan jarida duka. Ganau sun ce lamarin ya faru ne bayan ‘yan majalisar sun gama kada kuri’a kan bikin kewayowar ranar samun ‘yancin kan kasar. Masu kutsen sun shiga majalisar dauke da sanduna sannan suka tashi […]

Jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan kotun kolin Venezuela

Jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan kotun kolin Venezuela

Wani jirgi mai saukar ungulu ya jefa bam a ginin kotun kolin Venezuela, a wani mataki da shugaba Nicolas Maduro ya kira fa aikin ta’addanci. ‘Yan sanda sun ce wani jami’insu ne ya dauki jirgin helikofta, kana ya jefa gurneti ta sama kan kotun kolin kasar. Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta, sun […]