An sake kaddamar da kamfanin jirgin saman Najeriya a Birtaniya

Ministan Harkokin Sufurin Najeriya Sanata Hadi Sirika ya kaddamar da sabon kamfanin jirgin saman Najeriya a wani bikin baje kolin jiragen saman a kasar Birtaniya.

An sake kaddamar da kamfanin jirgin saman Najeriya a Birtaniya

Ya ce zuwa watan Disamban bana ake fatan kamfanin jiragen saman na Najeriya zai fara aiki. Har ila yau ya ce kamfanin zai rika zirga-zirga kashi uku a tsakanin kasashe 81, wanda ta kunshi ta cikin gida da yankin Afirka ta Yamma da kuma sauran kasashen duniya. “Najeriya za ta iya. Kuma muna so mu […]