Niger: Hana Kwararar Bakin Haure Ya Haifar Da Talauci

Tattalin arzikin yankin jihar Agadez a Jamhuriyar Nijar, na fuskantar koma baya sakamakon hana kwararar bakin hauren da hukumomi suka yi.

Niger: Hana Kwararar Bakin Haure Ya Haifar Da Talauci

Wasu ‘yan kasuwa da ke sayar da kayayyakin da bakin hauren ke amfani da su wajen ketara sahara, sun ce yanzu babu abin da suke fama da shi face yunwa da talauci, saboda ba ma su siyan kayan da suke sayarwa. ‘Yan kasuwar sun ce, yanzu babu abin da suke face zaman kashe wando a […]

Gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa

Daya daga cikin jami'an sojin Jamhuriyar Nijar a lokacin da yake gadin 'yan gudun hijira a yankin Diffa, da ke kudu maso gabashin kasar.

Gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin Diffa

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da tsawaita dokar ta bacin da ta kaddamar a yankin Diffa saboda ci gaba da barazanar tsaron da ake fuskanta a yankin. Sanarwar gwamnatin ya nuna cewar an tsawaita dokar ne daga yau 18 ga watan Satumba zuwa watanni 3 nan gaba. Zalika tawaita dokar ya shafi yankin dake makwabtaka […]

Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Juyar Da Kanmu – Wadanda Suka Tsira

Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai

Yadda ‘Yan Boko Haram Suka Juyar Da Kanmu – Wadanda Suka Tsira

Wani dan kungiyar Boko Haram da ake kira da kwamanda a tsakanin ’ya’yan kungiyar, ya yi ikirarin cewa shi ne ya jagoranci sace ’yan matan Chibok daga makaranta a shekarar 2014. ‘Kwamandan’ wanda aka gano sunansa Auwal Isma’il ne ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da ya yi da kafar labarai ta PRNigeria. Fiye […]

An Shirya Taron Fadakar Da Manoma Da Makiyayan Nijar

Rikicin manoma da makiyaya babbar matsala ce da ke yawan addabar kasashen nahiyar Afirka, lamarin da kan janyo hasarar rayuka da dumbin dukiyoyi. Hakan ya sa wata kungiya mai zaman kanta a Jamhuriyar Nijar d ake kira FRAPS ta shirya wani taron wayar da bangarorin biyu kan muhimmancin zaman lafiya.

An Shirya Taron Fadakar Da Manoma Da Makiyayan Nijar

Wata kungiya mai zaman kanta da ke bin diddigin harkar manoma da makiyaya da ake kira FRAPS a takaice, ta shirya wani taron bita da ya tattaro manoma da makiyayan Jmahuriyar Nijar domin a tattaunawa. Kungiyar ta tattaro bangarorin biyu ne daga jihohin Maradi da Damagaram da Diffa domin kara karfafa dangantakar da ke tsakaninsu […]

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Kan Iyakar Najeriya

Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun halaka mutane 15 suka kuma yi garkuwa da wasu mutane takwasa a wani kauye da ke kusa da iyakar Najeriya a yankin garin Kolofota na kasar Kamaru.

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 a Kan Iyakar Najeriya

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, sun harbe mutane 15 har lahira, kana suka yi garkuwa da wasu takwas a wani kauye da ke arewacin kasar Kamaru.Jami’ai sun ce ‘yan bidigar sun yi ta bude wuta ne akan kauyen Gakara da bindgogi masu sarrafa kansu, da tsakar daren Alhamis har zuwa […]

Majalisar Dokokin Jamus Ta Kai Ziyara Nijar Domin Tattaunawa Kan Harkokin Tsaro

Majalisar Dokokin Jamus Ta Kai Ziyara Nijar Domin Tattaunawa Kan Harkokin Tsaro

Mahimmancin kasar Nijar a yankin Sahel bisa harkokin tsaro ya sa Majalisar Dokokin kasar Jamus kai ziyarar tattunawa da ‘yan majalisar Nijar din. Kasar Nijar na yankin da masana harkokin tsaro suka bayyana na da mahimmanci wajen daukan matakan karya lagon kungiyoyin ta’addancin da suke cikin kasashen yankin Sahel. Mahimmancin ya ba da hujjar kafa […]

Nigeria Za Ta Fara Taso Keyar Masu Laifi Su Gudu UAE

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a wata yarjejeniyar da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), wadda za ta fadada yaki da cin hanci da gwamnatinsa take yi da tsaron kasa da kuma bunkasa tattalin arziki.

Nigeria Za Ta Fara Taso Keyar Masu Laifi Su Gudu UAE

Yarjejeniyar ta yi tanadin musayar mutanen da suka aikata manyan laifuka tsakanin Najeriya da Hadaddiyyar Daular Larabawa. Shugaban ya bayyana al’amarin da wani muhimmin ci gaba ga kasar wanda zai taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da tsaro da yaki da cin hanci da ciki da wajen kasar. Sabuwar yarjejeniyar za ta taimaka wajen tasa keyar […]

Nijar ta Daure ‘Yan Sanda Uku Da Suka Ba Dalibi Kashi

Wata Kotu a Nijar ta yankewa wasu ‘Yan Sanda uku hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda samunsu da laifin dukan wani dalibin jami’a lokacin da dalibai ke gudanar da zanga zanga a Niamey.

Nijar ta Daure ‘Yan Sanda Uku Da Suka Ba Dalibi Kashi

Wata Kotu a Nijar ta yankewa wasu ‘Yan Sanda uku hukuncin daurin shekara guda a gidan yari saboda samunsu da laifin dukan wani dalibin jami’a lokacin da dalibai ke gudanar da zanga zanga a Niamey. Kotun ta kuma umurci ‘Yan Sandan su biya tarra sefa miliyan 15 kwatankwacin yuro 23,000 ga dalibin da suka jikkata. […]

Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Jama'a daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga jinya ya kuma koma aiki, inda suke bayyana abinda suka fi so shugaban ya fi mayar da hankali a kai.

Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa ga ‘yan kasar mutane da dama suke ta bayyana ra’ayinsu kan abinda ya kamata ya fuskanta. A irin muhawarorin da ake ta yi, wasu sun bayyana ra’ayinsu kan abubuwan da shugaban ya kamata ya fuskanta da suka hada da tunkarar matsalar tsaro da kuma yajin […]