Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

A ranar Laraba ne kwale-kwale ɗauke da 'yan kasuwa 150 daga kauyen Gaya cikin jamhuriyar Nijar da ke kan hanyar zuwa kasuwa a garin Lolo a jihar Kebbi ya kife.

Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

An samu ceto mutane 50 daga cikinsu. Har yanzu ma’aitakan ceto daga jamhuriyyar Nijar da Najeriya na ci gaba da aikin ceton waɗanda suka rage. Sai dai babu tabbas cewa za’a same su a raye. A halin yanzu an kai wadanda aka ceto asibitin Lolo domin samun magunguna da kulawa. Jami’an hukumar bada agajin gaggawa […]