Nigeria: Kun san yadda Biafra ta samo asali?

Biafra wata kalma ce da masu fafutikar ballewa daga Najeriya a yankin Kudu maso Gabashin kasar suke amfani da ita wajen bayyana fatansu na ganin sun kafa kasar kansu wadda su kai wa lakabi da "Jamhuriyar Biafra".

Nigeria: Kun san yadda Biafra ta samo asali?

Sunan Biafra ya samo asali ne da gabar mashigin tekun Atlantic da ke yankin Kudu maso Gabashin kasar. Galibi mutanen da suke zaune a yankin ‘yan kabilar Igbo ne amma akwai wasu kabilu kamar Efik da Ibibio da Annang da Ejagham da Eket da Ibeno da kuma Ijaw. Kokarin ballewar yankin daga Najeriya shi ne […]

Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Ana samun alkaluma masu cin karo da juna na adadin mutanen da suka rasu sakamakon gobara a wata masana'antar iskar gas a garin Nnewi na jihar Anambra.

Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Hukumomin ‘yan sanda wadanda suka tabbatar da aukuwar gobarar, ba su yi karin haske ba dangane da adadin mutanen da suka kone ba. Hukumar agaji ta NEMA ta ce mutane biyar ne suka rasu a yayin da mutane bakwai suka samu raunuka. NEMA ta ce gidaje shida da motoci 22 ne suka kone sakamakon gobarar. […]

Jiragen Ethiopia sun fara tashi daga Kaduna

Jiragen Ethiopia sun fara tashi daga Kaduna

Kamfanin jirgin sama na kasar Habasha, Ethiopian Airline, ya fara tashi daga birnin Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya domin tafiyar kasa-da-kasa. A ranar Talata ne jirgin farko na kamfanin jiragen ya tashi daga Kaduna, lamarin da masu hanu da tsaki a harkar jiragen sama ke cewa zai taimaka wa mazauna birnin da wasu […]