Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Ana samun alkaluma masu cin karo da juna na adadin mutanen da suka rasu sakamakon gobara a wata masana'antar iskar gas a garin Nnewi na jihar Anambra.

Gobara ta hallaka rayuka a Anambra

Hukumomin ‘yan sanda wadanda suka tabbatar da aukuwar gobarar, ba su yi karin haske ba dangane da adadin mutanen da suka kone ba. Hukumar agaji ta NEMA ta ce mutane biyar ne suka rasu a yayin da mutane bakwai suka samu raunuka. NEMA ta ce gidaje shida da motoci 22 ne suka kone sakamakon gobarar. […]