Dangote ya sasanta tsakanin Hausawa da Yarbawa

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu da Basarake Oba na Ife, Oba Enitan Adeyeye Ogunlisi, sun kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin kabilun Hausawa da Yarbawa da ke garin na Ile-Ife.

Dangote ya sasanta tsakanin Hausawa da Yarbawa

Zaman dai ya zo a karkashin gidauniyar Dangote da ta bayar da sama da naira miliyan 50 ga al’ummar da rikicin kabilancin tsakanin Hausawa da Yarbawa ya shafa cikin watan Maris na bana. Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote na cikin masu halartar wannan taron sasantawar, inda ya bayar da wani tallafi ga matasan. Sama da […]