Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

A Najeriya sojojin kasar da dama na jibge a wasu yankuna domin gudanar da sintiri da atisaye, musamman domin kwantar da hankulan jama'a da kuma wanzar da zaman lafiya. Shin mene ne tasirin irin wannan sintiri?

Tasirin Sintirin Da Sojojin Najeriya Ke Yi a Sassan Kasar

 A sassa daban daban na Najeriya dakarun kasar kan gudanar da atisaye na musamman inda akan jibge su su yi kwana da kwanaki ko kuma su dauki wani tsawon lokaci suna atisayen. Akan kai dakarun ne yankunan da ke fama da wasu matsaloli na musamman, misali a yankin da ake fama da matsalar satar shanu […]