Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa kimanin rayuka hudu ne aka rasa a wani sabon rikici dake neman barkewa a tsakanin Fulani Makiyaya da kabilun yankin Kwateh a yankin karamar hukumar Girei.

Adamawa: Tashin Hankali Tsakanin Fulani Makiyaya Da ‘Yan Yankin Kwateh

An tabbatar da cewa rikicin na neman tashi ne biyo bayan kashe wasu Fulani makiyaya biyu, inda suma fulanin suka kashe wasu mutanen yankin biyu a wani harin daukar fansa. To sai dai tuni wannan lamarin yakai ga fara kona gidajen wasu Fulani makiyaya a yankin, kamar yadda shugaban karamar hukumar Girein Alhaji Hussaini Masta, […]