Buhari Ya Yi Kuskure da Korar Abdulrasheed Maina Daga Aiki -Lauya

Yayin da ake cigaba da cece-kuce game da sake korar tsohon shugaban kwamitin yin garambawul ga shirin fanshon Najeriya, Abdulrasheed Maina daga aiki, masana harkar sharia a kasar sun bayyana cewa akwai kuskure a korar da shugaba Buhari yayi

Buhari Ya Yi Kuskure da Korar Abdulrasheed Maina Daga Aiki -Lauya

Shi dai shugaba Buhari, a wani sakon da aka wallafa a shafin Shugaban kasar na Twitter, ya bada umurnin a kori Abdulrasheed Maina daga aiki nan take, a kuma yi bincike game da yadda aka yi ya koma aikin gwamnati. Har-ila yau shugaba Buhari ya umarci shugabar ma’aikatan gwamantin tarayya, Oyo-Ita Winifred Ekanem, da ta […]