Likitoci Na Cigaba da Yajin Aiki a Najeriya

Rahotanni daga Ibadan babban birnin jihar Oyo na nuni da cewa likitocin asibitin koyaswa ko UCH, asibitin koyaswa na farko a duk fadin kasar na cigaba da yajin aiki

Likitoci Na Cigaba da Yajin Aiki a Najeriya

Yau likitocin da ake kira Resident Doctors suka shiga rana ta biyu na yajin aikin da suka soma yi a duk fadin kasar. A asibitin koyaswa dake Ibadan babban birnin jihar Oyo, wato UCH, likitocin wurin na cigaba da yajin aiki kamar sauran ‘yanuwansu a kasar. Shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewa a fannoni daban […]

EFCC Ta Gano Naira Milyan 300 Cikin Wata 4 A Shiyyar Oyo.

Mataimakin shugaban hukumar a shiyyar kazeem Hussein ne ya bayyan ahaka a wani taron manema labarai.

EFCC Ta Gano Naira Milyan 300 Cikin Wata 4 A Shiyyar Oyo.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, shiyyar jahar Oyo ta gano Naira milyan 300 cikin watanni hudu da suka gabata. Mataimakin shugaban hukumar reshen jahar Oyo Kazim Hussein, shine ya bayyan haka lokacinda yake magana da manema labarai kan ayyukan hukumar a yankin. Mr. Kazeem yace cikin wadanda hukumar ta […]

Daruruwan ‘Yan Kungiyar Asiri Sun Shiga Hannu a Najeriya

Rudunar 'yan sandan jihar Oyo da majalisar jihar na daukar matakan kare jihar daga 'yan kungiyoyi asiri da suka zama ruwan dare a yankin.

Daruruwan ‘Yan Kungiyar Asiri Sun Shiga Hannu a Najeriya

WASHINGTON D.C. — A kokarin da ta ke yi na kare jihar Oyo, daga muggan ayyukan ‘yan kungiyar asiri da suka addabi makwabtan jihohin Lagos da Ogun, rudunar ‘yan Sandan jihar Oyo, ta kama daruruwan ‘yan kungiyoyin asiri domin hanasu afkawa jama’ar jihar. Kwamishinan ‘yan Sanda na jihar Abiodun Odude, ne ya shedawa taron ‘yan jarida […]

Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu a Najeriya

Hukumar kwastam din Najeriya na ci gaba da samun nasara akan masu fasakori, na baya bayan nan shine motoci goma sha biyar da hukumar ta kama a yankin jihohin Oyo da Osun shake da kaya iri iri da kudinsu ya haura Naira miliyan 28.

Hukumar Kwastam Ta Yi Babban Kamu a Najeriya

WASHINGTON D.C. — Shugaban kwastan mai kula da jihohin biyu Udu Aka shi ya gabatarwa taron ‘yan jarida ababen da suka kama wadanda inda ya ba da kiyasin kayan. Aka ya kara da cewa abun damuwa ne wasu ‘yan Najeriya marasa kishin kasa sun ki tuba da yin fasakorin kayayyaki duk da gargadin da ake yi […]