Pillars da Plateau United sun raba maki

Pillars da Plateau United sun raba maki

Kano Pillars da Plateau United sun raba maki daya-daya a tsakaninsu bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 33 a ranar Lahadi. Plateau United ce ta fara cin kwallo ta hannun Ibeh Johnson a minti na 17 da fara tamaula, kuma Pillars ta farke ta hannun Hamza Abba […]