Girgizar kasa ta hallaka sama da mutum 200 a Mexico

Wata mummunar girgizar kasa ta faru a tsakiyar birnin Mexico, inda ta hallaka mutane sama da 200, yayin da dama suka jikkata, wasu kuma ta rutsa su a cikin buraguzan gine-gine da suka rushe

Girgizar kasa ta hallaka sama da mutum 200 a Mexico

Girgizar wadda ta kai karfin lamba 7.1 a ma’aunin girgizar kasa, ta rushe gomman gine-gine, a babban birnin kasar, Mexico City, wadanda suka hada da wata makaranta, inda ake ganin ta rutsa yara a ciki. Tarin masu aikin sa-kai sun shiga taimaka wa masu aikin ceton gaggawa a kokarin da ake yi na gano masu […]