Odinga Na Son a Ba Sauran ‘Yan Takara Dama a Zaben Kenya

Shugaban adawar Kenya Raila Odinga ya gindaya wasu sharudda da ya ke so a amince da su kafin shiga sabon zaben shugaban kasar da za a yi ranar 17 ga watan gobe.

Odinga Na Son a Ba Sauran ‘Yan Takara Dama a Zaben Kenya

Odinga ya bukaci sake wasu daga cikin jami’an hukumar zaben da kuma gurfanar da wasu a gaban kotu saboda zargin tafka magudi da kuma bai wa daukacin jam’iyyun siyasar damar sanya ranar gudanar da zaben sabanin ranar da hukumar zabe ta sanar. Dan takarar ya kuma bukaci a ba daukacin ‘yan takarar shugaban kasar 8 […]

Kenyatta Ya Amince Da Hukuncin Kotun Koli

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya ce ya amince da matsayar da kotun kolin kasar ta dauka na soke nasarar zaben shugaban kasar da ya lashe, amma kuma ya ce wannan matsaya ta tauye hakkin al'umar kasar da suka zabe shi.

Kenyatta Ya Amince Da Hukuncin Kotun Koli

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya ce zai bi umurnin kotun kolin kasar, wacce ta soke nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar da aka yi a watan da ya gabata, duk da cewa shi a gashin kansa ya ce bai amince da matsayar kotun ba. Koda yake Kenyatta ya ce zai yi biyayya ga […]

Kotun Koli ta Kenya ta rushe zaben Shugaban Kasa

Kotun Koli ta Kenya ta rushe zaben Shugaban Kasa

Kotun Koli a kasar Kenya ta rushe zaben da aka gudanar a kasar Kenya wanda shugaba Uhuru Kenyatta ya lashe inda ta umarci da a sake gabatar da sabon zabe nan da kwanaki 60 masu zuwa. Rushe zaben dai ya biyo bayan korafin da bangaren ‘yan adawa ya shigar karkashin jagorancin Raila Odinga wanda ya […]

Zaben Kenya: Uhuru Kenyatta ya kayar da Raila Odinga

Zaben Kenya: Uhuru Kenyatta ya kayar da Raila Odinga

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Talata data gabata a kasar, a cewar hukumar zabe ta kasar. Mista Kenyata, wanda shine shugaba mai ci a yanzu sakamakon nasarar da ya samu a shekara ta 2003, ya samu kaso 54.3 na cikin dari na yawan kuri’un da aka kada, […]

A bayyana Odinga a matsayin ‘Shugaban Kasa’ – ‘Yan adawar Kenya

A bayyana Odinga a matsayin ‘Shugaban Kasa’ – ‘Yan adawar Kenya

Kasashen Burtaniya da Amurka sun bi sahun kasashen waje ‘yan sa ido na Kungiyar tarayyar Turai, Kungiyar Hadin kai ta Afirika, Kungiyar kasashe rainon Ingila da kuma Cibiyar Carter wajen kira ga shugabannin jam’iyyu da su kara hakuri da kuma kaucewa duk wani abu da zai harzuka fitina, kafin fadin babban sakamakon zabe da ake […]

Rikicin sakamakon zabe ya yi sanadin rai 4 a Kenya

Rahotanni Daga kasar Kenya sun ce mutane 4 aka kashe a tashin hankalin da ya biyo bayan kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar wanda ‘yan adawa ke zargin an tafka magudi.

Rikicin sakamakon zabe ya yi sanadin rai 4 a Kenya

            Bada sakamakon wucin gadi cewar shugaba Uhuru Kenyatta ke gaba wajen lashe zaben da kashi 54 ya haifar da cacar baki, inda ‘yan adawa tare da dan takarar su Raila Odinga mai kashi kusan 45 suka kekashe kasa cewar basu amince da sakamakon ba saboda an tafka magudi. Wannan […]

Kenya: Hukumar zabe ta musanta zargin yin kutse a na’urarta

Hukumar zaben kasar Kenya wato IEBC ta ce babu wani kutse da aka yi wa na'urorinta daga ciki ko waje a kowane lokaci a yayin zabukan.

Kenya: Hukumar zabe ta musanta zargin yin kutse a na’urarta

Shugaban hukumar ne dai ya fitar da wata sanarwa domin mayar da martani ga ikrarin da dan takatar shugaban kasa na jam’iyyar adawa Raila Odinga ya yi. Mr. Odinga – babban abokin karawar Shugaban Uhuru Kenyatta a zaben – ya yi zargin cewa masu kutse sun kutsa ciki na’urar da ke tattara sakamako suka sassauya […]

Zaben Kenya: Sakamakon farko ya nuna Kenyatta ya sha gaban Odinga

Zaben Kenya: Sakamakon farko ya nuna Kenyatta ya sha gaban Odinga

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya shiga gaba a yawan kuri’u a zaben kasar da aka yi ranar Talata. Alkalumman da hukumar zaben kasar ta fitar sun nuna cewa kawo yanzu an kidaya kashi 3/4 na yawan kuri’un da aka jefa kuma Shugaba Kenyatta ya samu kashi 55% daga cikinsu; yayin da babban abokin hammayarsa, […]