Buhari ya yi wa gwamnan Osun Rauf Aregbesola waya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira wo gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola ta wayar tarho inda ya yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifiyarsa Saratu Aregbesola.

Buhari ya yi wa gwamnan Osun Rauf Aregbesola waya

Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar Mallam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twiiter ta ce Shugaba Buhari, wanda ya kwashe sama da wata biyu yana jinya a London, ya yi wayar ne ranar Alhamis. Ya kara da cewa shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan Saratu Aregbesola. A cewar sanarwar, shugaban na Najeriya […]