China za ta haramta amfani da mota mai amfani da fetir

Kasar da aka fi cinikin motoci a duniya wato China, na shirin haramta kerawa da kuma sayar da motocin da suke amfani da man fetir da dizal.

China za ta haramta amfani da mota mai amfani da fetir

Mataimakin ministan masana’antu na kasar ya ce, tuni suka fara nazari na tsanaki, sai dai har yanzu ba su yanke shawarar lokacin da za a tabbatar da haramtawar ba. Xin Guobin ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na kasar cewa, “Wadannan matakai za su kawo sauyi wajen bunkasa kamfanonin motocinmu”. China ta kera mota miliyan […]