Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ikirarin da ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, ya yi cewar 'yan hamayya ne ke daukar nauyin kungiyar masu fafatukar kafa kasar Biafra ta IPOB ya nuna cewar har yanzu gwamnatin Buhari na ci gaba da yada farfaganda maimakon mayar da hankali kan aiki.

Banida Hannu a Daukar Nauyin IPOB — Jonathan

A wata sanarwar da Reno Omokri, mataimaki na musamman kan shafukan sadarwar zamani ga Shugaba Goodluck Jonathan, ya wallafa a shafin Facebook na tsohon shugaban kasar, cewa idan gwamnatin Najeriya ta san ‘yan hamayyar da ke daukar nauyin ‘yan IPOB, ta kama su tare da gurfanar da su gaban kotu. Mista Jonathan ya ce bai […]