Gwamnatin Buhari ‘Ta Kai Karar Mutum 6,646 Kotu a Shekara Daya’

Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi karar mutum 6,646 a kotu bisa aikata laifuka daban-daban a tsakanin shekarar shari'a ta 2015-2016.

Gwamnatin Buhari ‘Ta Kai Karar Mutum 6,646 Kotu a Shekara Daya’

Wata sanarwa da kakakin ministan shari’a Abubakar Malami, ya aikewa manema labarai ta ce 325 cikin laifuka 1,330 kanane. Kakakin, Comrade Salihu Othman Isah, ya ce an yanke hukuncin da ya goyi bayan gwamnati kan kashi 90 cikin dari na karar da ta shigar. Ya kara da cewa gwamnati ta yi tsimin sama da N119 […]