Nijeriya Za Ta Cigaba Da Zama Kasa Daya Mai Manufa Guda…. – Sultan

Nijeriya Za Ta Cigaba Da Zama Kasa Daya Mai Manufa Guda…. – Sultan

Sokoto – Maigirma Sarkin Musulmi, Ahaji Sa’ad Abubakar ya roki ‘yan Nijeriya su zauna lafiya da kowa su kuma kauracewa duk wani abun da zai yi barazana ga zaman lafiyar da ke akwai tsakanin mabanbanta kabilu. Sarkin musulmin yayi wannan  kiran a wata sanarwa da Sakataren Majalisar Daular, Alhaji Umar Ladan ya fitar ranar Jumma’a […]

Sarkin Musulmi Ya Jaddada Mahimancin Zaman Lafiya

A jawabinsa wa al'ummar Musulmi bayan saukowa daga babbar sallah, Mai Martaba Sarkin Musulmi ya tabo batun rarrabuwan kawunan 'yan Najeriya da barazanar da hakan ke yiwa kasar kana ya jaddada mahimmancin zaman lafiya.

Sarkin Musulmi Ya Jaddada Mahimancin Zaman Lafiya

Babban abun da ya fi daukan hankalin Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar III a jawabinsa na babban sallah wa Musulman Najeriya shi ne irin halin da kasar Najeriya ke ciki da kalubalen rarrabuwan kawunan ‘yan kasar. Yana mai cewa kwanakin baya an samu kalamun rarrabuwa daga mutane daban daban daga sassan kasar. Ana cewa mutane […]

Sultan Ya Tabbatar Cewa 1 Ga Watan Satumba Ita Ce Ranar Sallah

Sultan Ya Tabbatar Cewa 1 Ga Watan Satumba Ita Ce Ranar Sallah

Mai Girma Sarkin Musulmi, Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addini Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar ya tabbatar da cewa 1 ga watan Satumba, 2017 ce ranar Babbar Sallah. Wannan bayanin na kunshe cikin takardar da Prof. Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bada shawarwari kan harkokin Addini ta Daular Musulunci dake Sokoto ya sakawa hannu. Sakon […]

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

An cimma sulhu a sabanin da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar III da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

Zaman ya biyo bayan kwashe kwanaki da wasu manyan sarakunan arewacin Najeriya suka yi suna kokarin sasanta manyan sarakan biyu. Sulhun ya kai zangon karshe ne ranar Asabar da wani zaman da aka yi a birnin Sakkwato. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daya daga cikin manyan sarakuna biyu da suka jagoranci wannan sulhun […]

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

An fara sulhunta wani sabani da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad a Najeriya da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

A ranar Litinin ne dai magajin gari ya fice a fusace daga wani zaure da suke ganawa da Sarkin kuma ya sanar da yin Murabus daga kan mukamin wanda ya rike tsawon shekara 20. Magajin garin dai ya yi zargin cewa sarkin ya ci masa zarafi a wajen wani sulhu da ake tsakaninsa da wani […]

Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

  Tun a ‘yan watannin baya ne dai takaddama ta barke tsakanin  Magajin garin na Sokoto da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III, bisa nadin sarautar Marafan Sokoto, da mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi wa Alhaji Inuwa Abdulkadir, tsohon Ministan Wasanni da Matasa. Kan wannan al’amari ne tsohon Magajin gari mai […]

Sarkin Musulmi Yayi Kira Ga ‘Yan Kasar Su Dubi Kasashen Da Ake Rikici

Sarkin Musulmi Yayi Kira Ga ‘Yan Kasar Su Dubi Kasashen Da Ake Rikici

Mai Alfarma ya bada wannan shawarar ce lokacinda yayi buda baki da shugabannin hukumomin tsaro dana kabilu. Mai-alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad na 3, yayi kira ga ‘yan Najeriya su dage wajen tabbatar da ganin kasar ta ci gaba da zama lafiya, saboda duk wani abu sabanin haka ba Alheri bane ga kasa da […]