Turkiyya ta saki sautin kisan Kashoggi

Turkiyya ta saki sautin kisan Kashoggi

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya bayyana cewar ya kasar sa ta baiwa kasashen Amurka, Birtaniya, Jamus da Saudiya sautin kisan dan jaridar nan mai sharhi Jamal Khashoggi dan kasar Saudi Arabiya. Shugaban na Turkiyya Erdogan ya sake nanata cewar Saudiya ta san wadanda suka kashe Jamal Khashoggi. Jamal Khashoggi dai ya kasance fitaccen […]

Snapchat Ta Toshe Al-Jazeera A Saudiyya

Kafar sadarwa ta Snapchat ta toshe kafar yada labarai ta Al Jazeera a kasar Saudiyya.

Snapchat Ta Toshe Al-Jazeera A Saudiyya

Snapchat ya dauki matakin ne bisa umarnin da hukumomin Saudiyya suka ba da na cire baki daya kafar yada labaran mallakar kasar Qatar, saboda kasar ta bijirewa umarnin kasashen Labarawa da ke yankin Gulf da hakan ya sabawa dokokin kasashen. Qatar dai na takun saka da Saudiyya da wasu kasashen Larabawa da suka hada da […]

Alhazan duniya sun fara aikin Hajji a yau

Maniyyata na fuskantar kalubalen sauke farali, inda Saudiyya kuma ke fuskantar kalubalen samar da yanayi mafi kyau da ingantaccen tsaro ga maniyyatan.

Alhazan duniya sun fara aikin Hajji a yau

Maniyyata fiye da miliyan biyu ne ake sa ran za su fara zaman Mina daga ranar Larabar nan, a wani bangare na ibadar aikin hajjin bana tsawon kwana biyar a kasar Saudiyya. Dubban daruruwan maniyyata musulmi na ta isa Saudiyya daga sassa daban-daban na duniya domin aikin hajjin, ciki har da maniyyatan kasar Iran, bayan […]

Saudi Arabia: An Kama Yaron Da Ya Yi Rawar ‘Macarena’

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama wani yaro mai shekara 14 wanda aka nuna a wani bidiyo yana taka rawar wakar 'Macarena' a kan titi.

Saudi Arabia: An Kama Yaron Da Ya Yi Rawar ‘Macarena’

Bidiyon ya ja hankulan dubban mutane a Twitter. Hukumomi na yi wa yaron tambayoyi bayan an zarge shi da “nuna rashin tarbiyya” a birnin Jeddah, in ji wata sanarwa. Ba a tabbatar da ko yaron dan kasar ta Saudiyya ne ba, kuma ko hukuma za ta gurfanar da shi a kotu. A farkon wannan watan […]

Saudiyya Ta Bai Wa ‘yan Nigeria da Aka Ci Zarafinsu Diyyar N1m

Gwamnatin Saudiyya ta nemi afuwar wasu mahajjatan Najeriya biyu da jami'an tsaro suka ci zarafinsu a filin jirgin sama na Madina.

Saudiyya Ta Bai Wa ‘yan Nigeria da Aka Ci Zarafinsu Diyyar N1m

Mataimakin gwamnan yankin Madina, Sheikh Mohammad Albijawi, wanda ya mika wa wadanda abin ya shafa wasikar, ya tabbatar musu da cewar za a hukunta jami’an tsaron da suka aikata laifin. Saudiyyar ta kuma bai wa mutanen diyyar riyal dubu biyar ga ko wanne daya daga cikinsu, wanda ya kama naira dubu 500 kenan ga duk […]

Wasu Mahajjata Tara Sun Isa Madina a Keke Daga London

Wasu mahajjatan Birtaniya su tara sun isa birnin Madinah na Saudiyya a keke, bayan sun yi tafiyar kilomita 3,000 daga London.

Wasu Mahajjata Tara Sun Isa Madina a Keke Daga London

Hukumomin Saudiyya sun tarbi mutanen a Madina cike da murna da jinjina a gare su. Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruwaito cewa kungioyin masu tseren kekuna na Madinah da Taibah ne suka tarbi mahajjatan karkashin jagorancin hukumar wasanni ta Saudiyya, inda aka dinga yi musu kade-kade da watsa musu furanni don […]

Sa’udiyya Ta Bude Iyakokinta Ga Mahajjatan Qatar

Sarki Salman na Sa'udiyya ya bada umarnin bude iyakar kasar da Qatar don bayar da dama ga Mahajjatan da za su shiga kasar don gudanar da ayyukan hajjinsu a bana duk da rikicin diflomasiyar da ke tsakaninsu. Tuni dai Qatar ta yi marhabun da matakin wanda ta bayyana a matsayin ci gaba da tskaninta da Sa'udiyyar la'akari da takun sakar dake tsakani.

Sa’udiyya Ta Bude Iyakokinta Ga Mahajjatan Qatar

Sanarwa sake bude iyakokin kasar domin bai wa mahajatta damar ketarawa zuwa Sa’udiyya, shi ne sassauci irinsa na farko da Qatar ke samu tun bayan fara takun-saka da kasashen na yankin Golf 4 da suka kakaba mata takukumai bayan katse huldar diflomasiya da ita. Sarkin Salman ya ce bayan iyakokin kasa, saudiya za kuma ta […]

Ko masarautar Saudiyya na da hannu a batan ‘ya’yanta?

Ko masarautar Saudiyya na da hannu a batan ‘ya’yanta?

Da sanyin wata safiya a ranar 12/06/2003, aka tasa keyar daya daga cikin Yariman wajen birnin Geneva. Sunansa Sultan bin Turki yarima Abdulaziz bin Fahd, ya gayyace shi cin abincin safe. Abdulaziz ya roki Sultan ya koma gida Saudiyya, inda ya shaida masa za a magance kace-nacen da ake yi kan sukar da ya ke […]

An kama wani mawaki kan yin rawar dab a Saudiyya

An kama wani sanannen mawaki a Saudiyya saboda yin rawar dab yayin wani taron rawa da waka a a kudu maso yammacin kasar.

Abdallah Al Shahani, wani mai gabatar da shiri a talbijin, jarumin fina-finai, kuma dan asalin kasar Saudiyya, ya yi rawar ne wacce ake rufe goshi a dan rankwafa a yayin wani taron wakoki da aka yi a birnin Taif cikin karshen makon da ya gabata. An haramta rawar dab a kasar, saboda hukumomi na ganin […]

Turkiyya ta tsoma baki kan rikicin Qatar da Saudiyya

Shugaban Turkiyya zai fara wata ziyarar kwana biyu a yankin Gulf, kan kokarin dinke barakar da ta sanya wasu kasashen larabawa suka juya wa kasar Qatar baya.

Turkiyya ta tsoma baki kan rikicin Qatar da Saudiyya

Racep Tayyip Erdogan zai fara isa kasar Saudiyya wadda ita ce jagaba kan zargin Qatar na taimaka wa ‘yan ta’adda, kafin daga bisani kuma ya shiga kasar Kuwait wadda ta ke matsayin mai shiga tsakanin a rikicin sannan kuma ya kare ziyarar tasa a Qatar. A watan Yuni ne kasashen Saudiyya da Hadaddiyar daular larabawa, […]