Sanata Shehu Sani ya fice daga Jam’iyya APC

Sanata Shehu Sani ya fice daga Jam’iyya APC

Sanata Shehu Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya sanar da ficewa daga Jam’iyyar APC. Sanata Sani wanda ya mika takaddar ficewa daga Jam’iyyar ga shugaban Jam’iyyar na kasa Komared Adams Oshimole bai sanar da dalilin ficewar tasa ba, bugu da kari bai bayyana Jam’iyyar da zai koma ba.

Yunkurin Jihar Kaduna Na Ciwo Bashi Ya Haddasa Yamutsi

Jihar Kaduna na cikin jihohin da suke neman ciwo bashi amma wannan lamarin ya rarraba kawunan ‘yan jihar inda har mata suka fito suna zanga zanga tare da dorawa Senator Shehu Sani laifin kawo cikas ga yunkurin

Yunkurin Jihar Kaduna Na Ciwo Bashi Ya Haddasa Yamutsi

Yunkurin gwamnatin jihar Kaduna na ciwo bashi domin gudanar da wasu ayyuka na ci gaba da rarraba kawunan ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar. Wasu mata da suka dorawa Senator Shehu Sani alhakin jawo jinkirin ciyo bashin sun fito sun yi zanga zanga a garin Kaduna, babban birnin jihar. Daya daga cikin matan da suka […]

‘Son zuciya ne ya hada El-Rufa’i da Shehu Sani a Kaduna’

A kwanakin baya ne kungiyar 'yan jarida ta Najeriya NUJ ta yi Allah-wadai bisa wani hari da wasu 'yan dabar siyasa suka kai a sakatariyar 'yan jarida da ke Kaduna yayin wani taron manema labarai.

‘Son zuciya ne ya hada El-Rufa’i da Shehu Sani a Kaduna’

Wasu yan majalisar dattijan jihar ne suka kira taron manema labarai domin nuna damuwa a bisa yadda al’amura a jami’ar APC ke tafiya. Manyan ‘yan siyasar jihar sun zargi gwamnatin jihar da shirya harin, sai dai gwamnatin ta musanta zargin kuma ma har Allah-wadai ta yi da wadanda suka kai shi. Sanata Shehu Sani, wanda […]

An tarwatsa taron APC a Kaduna

An samu hatsaniya a sakatariyar 'yan jarida da ke jihar Kaduna yayin da wasu sanatocin jam'iyyar APC ke taro da manema labarai, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

An tarwatsa taron APC a Kaduna

“Wadansu mutane ne dauke da makamai suka kai hari cibiyar ‘yan jarida da ke kan hanyar Muhammadu Buhari Way (Waff Road) ranar Lahadi,” a cewar rahotanni. Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hukunyi da kuma wasu ‘yan siyasa jihar ne suka kira taron manema labaran. “Yau (Lahadi) a sakatariyar ‘yan jarida da ke Kaduna muna […]

‘Masu fuska biyu a gwamnatin Buhari ne kuraye’

Cece-kucen da kalaman sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na facebook na ci gaba da daukar dumi, musamman ganin uwar gidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wato Aisha Buhari ta yi amfani da hakan wajen maida martani ga 'yan kasar.

‘Masu fuska biyu a gwamnatin Buhari ne kuraye’

Wasu dai sun fusata da kiransu kananan dabbobi da Sanatan ya yi, inda shi kuma abin da ya ke nufi da hakan shi ne talakawa. Sai dai ya ce sun yi masa mummunar fahimta ne. A wata hira da Sulaimanu Ibrahim Katsina na sashen Hausa, sanatan ya ce ya yi wannan shagube ne bi sa […]

Ana daf da wancakali da Kuraye da Diloli daga Gwamnati – Aisha Buhari

Ana daf da wancakali da Kuraye da Diloli daga Gwamnati – Aisha Buhari

Uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari ta ce an kusa korar Kuraye da Diloli daga Gwabnatin Buhari. Aisha Buhari ta fadi wannan maganar ne a shafinta na Facebook ranar litinin inda ta yi amafani da abinda Sanata Shehu na jihar Kaduna ya rubuta yana habaici ga wasu ‘yan siyasa. Uwargida Aisha ta fadi wannan maganar ne […]