Watanni hudu da suka gabata ne kungiyar ‘yan Shiya reshen jihar Kano ta gurfanar da gwamnatin Kano da kwamishanan ‘yan sandan jihar da kwamishanan shari’a na jihar gaban babbar kotun tarayya dake Kano

Watanni hudu da suka gabata ne kungiyar ‘yan Shiya reshen jihar Kano ta gurfanar da gwamnatin Kano da kwamishanan ‘yan sandan jihar da kwamishanan shari’a na jihar gaban babbar kotun tarayya dake Kano

Kungiyar na zargin wadanda ta gurfanar da cin zarafin da kuma kisan gilla da ta ce sun yiwa ‘ya’yanta yayinda suke tattaki zuwa garin Zaria a watan Maris din bara. A cewar kungiyar matakin da jami’an tsaro suka dauka akan ‘ya’yanta tamkar tauye hakkinsu ne na gudanar da addinin da suke so. Kungiyar ta ce […]

Matan Kungiyar Shi’a Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Data Saki El-Zakzaky

Matan Kungiyar Shi’a Sun Bukaci Gwamnatin Tarayya Data Saki El-Zakzaky

Tsagin Mata na Kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi (IMN) sun gabatar da wata zanga-zangar lumana a Abuja inda sukayi kira ga hukumomi da su saki shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky. An gudanar da zanga-zangar ne a hedikwatar Hukumar Kare ‘Yancin Dan Adam ta Kasa Lokacin da take magana da sashin Hausa na BBC Mrs Maimuna Bintu […]

Kotu ta yi watsi da karar ‘yan Shi’a

Wata Kotun tarraya a jihar Kadunan Najeriya ta yi watsi da karar da jagoran kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da 'yan Shi'a, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya shigar kan sojin kasar.

Kotu ta yi watsi da karar ‘yan Shi’a

Zakzaky ya shigar da karar ne domin neman diyya bayan soji sun kashe daruruwan mabiyansa tare da lalace kadarorinsa a watan Disambar shekarar 2015. Sai dai alkalin kotun, Mai Shari’a Salisu Sha’aibu, ya ce kotun ta yi wasti da karar ne saboda ba ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka shigar ba. […]

Saudiyya ta daƙile kai hari Masallacin Ka’aba

Saudiyya ta daƙile kai hari Masallacin Ka’aba

Ƙasar Saudiyya ta ce ta daƙile wani “yunƙurin harin ta’addanci” da aka so kai wa Masallacin Harami a Makkah – wurin ibada mafi tsarki ga Musulmi. Wani ɗan ƙunar-bakin-wake ya tarwatsa kansa lokacin da dakarun tsaro suka zagaye ginin da yake ciki, in ji ma’aikatar harkokin cikin gida. Ginin ya ruguje, inda ya jikkata mutum […]