Matar Da Aka Sace Da ‘Yarta A Sokoto An Same Su A Kaduna

Matar Da Aka Sace Da ‘Yarta A Sokoto An Same Su A Kaduna

Lokaci ne na jimami ga iyalan wata matar aure mai shekaru 26, mai suna Sa’adatu Umar Abubakar, inda ranar Litinin 4 ga watan Satumbar shekarar da muke ciki ta 2017 aka sace matar da ‘yarta a Sokoto kan hanyar su ta zuwa bikin radin suna a gidan wasu ‘yan uwansu dake cikin garin na Sokoto. […]

Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

A ranar Laraba ne kwale-kwale ɗauke da 'yan kasuwa 150 daga kauyen Gaya cikin jamhuriyar Nijar da ke kan hanyar zuwa kasuwa a garin Lolo a jihar Kebbi ya kife.

Jirgin ruwa ya kife da mutum 150 a Kebbi

An samu ceto mutane 50 daga cikinsu. Har yanzu ma’aitakan ceto daga jamhuriyyar Nijar da Najeriya na ci gaba da aikin ceton waɗanda suka rage. Sai dai babu tabbas cewa za’a same su a raye. A halin yanzu an kai wadanda aka ceto asibitin Lolo domin samun magunguna da kulawa. Jami’an hukumar bada agajin gaggawa […]

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Ministan sufuri Amaechi ya fada a Sokoto gwamnatin tarayya na shirin hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo irin na zamani

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Kokarin gwamnatin tarayyar Najeriya na hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo ba zai tabbata ba sai da amincewar Majalisar Dattawa a cewar ministan sufurin kasar. A cewarsa tuni gwamnati ta tura bukatar zuwa majalisar. Rotimi Amaechi wanda shi ne ministan sufuri a karkashin shugabanci Muhammad Buhari yace jihohin uku da ake son […]

An gano daliban ‘boge’ 706 a Sokoto

An gano daliban ‘boge’ 706 a Sokoto

Gwamnatin Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta gano daliban boge 706 da suka yi yunkurin samun tallafin karatu daga asusun jihar. Wani kwamiti da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan hakikanin adadin daliban da suka cancanta a bai wa tallafin karatu ne ya gano hakan. Kwamitin, wanda Ambassador Shehu […]

NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

NDLEA ta kama kilogaram 881.100 na kwayoyi a Sokoto

Hukumar Yakin da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) tare da sauran hukumomi sun sami nasarar kwace wasu haramtattun kwayoyi da yawansu ya kai kilogaram 881.100, sakamakon wani sumamen hadin gwiwa na musamman da aka gudanar a Jihar Sokoto da kuma wasu yankuna tsakanin bodar Najeriya da Nijar. Shugaban hukumar, Kanar Muhammad Mustapha Abdallah (Mai […]

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

An cimma sulhu a sabanin da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar III da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

An sasanta sabanin masarautar Sokoto

Zaman ya biyo bayan kwashe kwanaki da wasu manyan sarakunan arewacin Najeriya suka yi suna kokarin sasanta manyan sarakan biyu. Sulhun ya kai zangon karshe ne ranar Asabar da wani zaman da aka yi a birnin Sakkwato. Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu yana daya daga cikin manyan sarakuna biyu da suka jagoranci wannan sulhun […]

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

An fara sulhunta wani sabani da ya kunno kai tsakanin Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad a Najeriya da daya daga cikin manyan 'yan majalisarsa, wato Magajin garin Sakkwato Alhaji Hassan Danbaba.

Za a sasanta Sarkin Musulmi da dan uwansa

A ranar Litinin ne dai magajin gari ya fice a fusace daga wani zaure da suke ganawa da Sarkin kuma ya sanar da yin Murabus daga kan mukamin wanda ya rike tsawon shekara 20. Magajin garin dai ya yi zargin cewa sarkin ya ci masa zarafi a wajen wani sulhu da ake tsakaninsa da wani […]

Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

  Tun a ‘yan watannin baya ne dai takaddama ta barke tsakanin  Magajin garin na Sokoto da fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar na III, bisa nadin sarautar Marafan Sokoto, da mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi wa Alhaji Inuwa Abdulkadir, tsohon Ministan Wasanni da Matasa. Kan wannan al’amari ne tsohon Magajin gari mai […]