‘Masu fuska biyu a gwamnatin Buhari ne kuraye’

Cece-kucen da kalaman sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na facebook na ci gaba da daukar dumi, musamman ganin uwar gidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wato Aisha Buhari ta yi amfani da hakan wajen maida martani ga 'yan kasar.

‘Masu fuska biyu a gwamnatin Buhari ne kuraye’

Wasu dai sun fusata da kiransu kananan dabbobi da Sanatan ya yi, inda shi kuma abin da ya ke nufi da hakan shi ne talakawa. Sai dai ya ce sun yi masa mummunar fahimta ne. A wata hira da Sulaimanu Ibrahim Katsina na sashen Hausa, sanatan ya ce ya yi wannan shagube ne bi sa […]