Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Jama'a daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga jinya ya kuma koma aiki, inda suke bayyana abinda suka fi so shugaban ya fi mayar da hankali a kai.

Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa ga ‘yan kasar mutane da dama suke ta bayyana ra’ayinsu kan abinda ya kamata ya fuskanta. A irin muhawarorin da ake ta yi, wasu sun bayyana ra’ayinsu kan abubuwan da shugaban ya kamata ya fuskanta da suka hada da tunkarar matsalar tsaro da kuma yajin […]