Wata Halitta Da Ba’a Taba Gani Ba Ta Bulla a Amurka

An gano wata halittar ruwa mai dogayen hakora wadda ba a taba gani ba bayan guguwar Harvey a Amurka.

Wata Halitta Da Ba’a Taba Gani Ba Ta Bulla a Amurka

Wata mata mai suna Preeti Desai ta ga wannan halittar a gabar tekun Texas kuma ta sa hoton a shafin Twitter, tana neman agajin tambayoyi. Matar ta tura hotuna da yawa sai ta rubuta, ”To masan ilimin halittu na Twitter, mene ne wannan?” Wannan na daya daga cikin halittu tara na kasar Indiya wadanda ba […]

Trump Zai Sake Kai Ziyara Texas

A karo na biyu cikin mako guda, shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa, Melania Trump za su sake kai ziyara jihar Texas domin jajintawa mutane da kuma ganewa idununsu yadda guguwar Harvey ta yi barna a yankin.

Trump Zai Sake Kai Ziyara Texas

Yayin da yake shirin kai ziyara birnin Houston da ambaliyar ruwa ta mamaye a jihar Texas, shugaba Donald Trump ya aika da wasika zuwa majalisar dokokin Amurka, yana neman kusan Dala biliyan 8, wadanda za a yi amfani da su domin tallafawa jihohin Texas da Louisiana. Ana sa ran, wannan bukata da shugaban ya gabatar […]

An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Hukumomin Houston a Amurka sun kafa dokar hana fitar dare domin magance matsalar satar kayan jama’a da ake samu sakamakon ambaliyar da ta mamaye birnin yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan agaji.

An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Magajin Garin Houston Sylvester Turner ya sanar da kafa dokar hana fitar daren da zata fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa karfe 5 na asuba. Turner ya ce suna da dubban mutanen da suka bar gidajen su domin samun mafaka a sansanonin da aka tanada, amma bata-gari na amfani da damar wajen fasa […]

Sai Inda Karfinmu Ya Kare Wajen Taimakawa Al’umar Texas – Trump

Al'umar jihar Texas da bala'in ambaliyar ruwa ya afkawa, na ci gaba da samun tabbaci daga hukumomin kasar kan tallafa masu da za a yi domin su koma rayuwarsu ta da yayin da shugaba Donald Trump ya ce har ya fara magana da wasu 'yan majalisar dokokin kasar.

Sai Inda Karfinmu Ya Kare Wajen Taimakawa Al’umar Texas – Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin agaza wa mutanen Texas da Louisiana domin ganin sun samu saukin bala’in da ya auka musu na ambaliyar ruwa. Shugaba Trump ya shaidawa taron ‘yan jarida a Fadar White House jiya Litinin cewa wadanda wannan lamari ya rutsa da su, su kwana da sanin cewa za su samu […]

Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Afkawa Birnin Houston Dake Amurka

Kamar yadda jami'ai a jihar suka nuna Houston na cikin juyayi bayan shaida wata babbar guguwa mai tafe da ruwa a cikin tarihin jihar Texas.

Bala’in Ambaliyar Ruwa Ya Afkawa Birnin Houston Dake Amurka

An shaida saukar ruwan sama mai yawan centimita 75, yayin da guguwar hurricane harvey ke ratsawa ta koguna – al’amarin da ya janyo ambaliyar ruwa a kan hanyoyi ya mayar da titunan birnin kamar koguna. Ana dai hasashen cewa cikin wannan makon a bana yankin zai shaida saukar ruwan sama mai yawa. An rawaito cewa […]

Mummunar Guguwa Ta Juye Ambaliyar Ruwa a Texas

Sama da mutum dubu guda aka tseratar daga yankunansu bayan mahaukaciyar guguwar nan da ta afkawa jihar Texax a Amurka ta haifar da kakkarfan ruwan saman daya juye zuwa ambaliyar ruwa a Houston.

Mummunar Guguwa Ta Juye Ambaliyar Ruwa a Texas

A cewar hukumar kula da yanayi ta kasar, karfi da kuma yawan ambaliyar ruwan kan ma’aunin centi mita 50 ba kakkautawa ya dakatar da zirga-zirga tare da sanya razani a zukatan mutanen yanki, lamarin daya tilasta kwashesu don kare lafiyarsu. Haka kuma yawan ruwan saman ya sanya koguna da dama yin ambaliya a yankin abin […]