Nigeria: Wata sabuwar cuta ta ‘kashe’ yara 50 a Jigawa

Rahotanni daga jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun ce a kalla yara 50 ne suka mutu a kauyen Gidan Dugus da ke karamar hukumar Dutse, sakamakon bullar wata cuta da ba a gane ta ba.

Nigeria: Wata sabuwar cuta ta ‘kashe’ yara 50 a Jigawa

Wasu kafafen yada labarai na yankin sun ce yaran sun mutu ne cikin makonni hudu zuwa biyar da suka gabata. Wani dan jarida da ke yankin ya shaida wa BBC cewa dagacin kauyen da al’amarin ya faru, ya tabbatar masa da faruwar lamarin. Ya ce yaran da suka mutun duk sun fito daga kauyen na […]