EFCC ta kwato ‘naira biliyan 329 daga kamfanonin mai’

Hukumar yaki da cin hanci da rshawa ta Najeriya EFCC, ta ce ta kwato kimanin naira biliyan 329 ($1.4 biliyan) da wasu kamfanonin mai suka karkatar tare da hadin gwiwar kamfanin mai na kasa na NNPC.

EFCC ta kwato ‘naira biliyan 329 daga kamfanonin mai’

Wata sanarwar da ta fitar ta kara da cewar an kwato kudaden ne tsakanin Yulin 2016 zuwa watan Yulin 2017 bayan wani korafi da ta samu kan zargin aikata ba daidai ba. Hukumar ta ce bincike ya nuna cewar kamfanonin sun karbi mai da yawa daga gwamanti ba tare da biyan kudi yadda ya kamata […]