Shugaba Buhari na Ganawa da Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar a Fadarsa

Shugaba Buhari na Ganawa da Manyan Hafsoshin Tsaron Kasar a Fadarsa

Yanzu haka shugaba Muhammadu Buhari na ganawa da Manyan Hafsoshin kasar da sauran Shugabanin tsaron kasar a fadarsa gwamnati dake Aso Rock a Abuja Ana gudanar da taron ne a ofishinsa dake cikin gidan shugaban kasa. Wadanda suke halartar taron sun hada da Ministan tsaro, Shugaban Hukumar tsaro, Babban Hafsan Sojan Tsaron Kasar, Babban Hafsan […]

Boko Haram: Shugabannin sojin Nigeria sun koma Maiduguri

Manyan hafsoshin sojin Najeriya sun isa birnin Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar domin tunkarar wani gagarumin shiri na yakar kungiyar Boko Haram.

Boko Haram: Shugabannin sojin Nigeria sun koma Maiduguri

  A makon da ya gabata ne Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo ya umarce su da su koma can bayan wani mummunan hari da kungiyar ta kai wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 40. Mai magana da yawun rundunar sojin kasa Birgediya Janar Usman Kuka-Sheka ya shaida wa BBC cewa da sanyin safiyar ranar […]

An kara wa sojojin da ke yaki da Boko Haram mukami

An kara wa sojojin da ke yaki da Boko Haram mukami

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar-Janar TY Buratai ya sanar a ranar Talata cewa ya amince da karin girma ga sojoji 6,199 da ke aiki da runduna ta musamman, Lafiya Dole, wadda ke yaki da kungiyar Boko Haram. Wata sanarwa da mataimakin daraktan watsa labarai na runduna ta bakawai ta sojin kasar Laftanar Kanar […]

Buratai Na Son Shekau A Mace Ko A Raye

Shugaban Sojojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai ya bawa Operation Lafiya Dole wa'adin kwanaki 40 ta kawo masa Shekau a mace ko a raye.

Buratai Na Son Shekau A Mace Ko A Raye

A ranar juma’a 21, ga watan yuli, shugaban rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya umurci shugaban rundunar dake yaki da boko haram ta Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru wa’adin kwanaki arba’in ya kawo masa shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar shekau a mace ko a raye. Mai magana da yawun rundunar […]

Mayakan Boko Haram ‘700 sun mika wuya’

Mayakan Boko Haram ‘700 sun mika wuya’

Mayakan kungiyar Boko Haram 700 ne suka mika wuya ga dakarun Najeriya, kamar yadda rundunar sojojin kasar ta yi ikirari. A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce mika wuyan ya biyo bayan farmakin da dakarun Najeriya suka kai ranar Litinin. Har ila yau, Kukasheka […]

Muna nan muna ƙoƙarin kamo Shekau – Buratai

Muna nan muna ƙoƙarin kamo Shekau – Buratai

Dakarun sojin Nijeriya sun ce suna can suna ƙoƙari don su kama shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau. Babban hafsan sojan ƙasar, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai ya ce ko da yake, ba zai iya bayyana dabarun da suke ƙoƙarin yin amfani da su a nan gaba ba, amma za su ci gaba da kutsa […]