Myanmar ‘Yan Kabilar Rohingya 37,000 Sun Tsere Cikin Awanni 24’

'Yan kabilar Rohingya mafi akasarinsu Musulmi, suna turereniyar samun abinci, bayanda suka tsere zuwa Bangladesh.

Myanmar ‘Yan Kabilar Rohingya 37,000 Sun Tsere Cikin Awanni 24’

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla ‘yan Kabilar Rohingya mafi akasarinsu Musulmi dubu talatin da bakwai ne, (37,000) suka tsere zuwa kasar Bangladesh cikin awanni 24, lamarin da ta bayyana shi a matsayin gudun hijira mafi girma da aka taba gani cikin karamin lokaci tun bayan sabon tashin hankalin da ya barke a kasar Myanmar. […]