Mata sun yi kira da a kauracewa shafin Twitter

Mata sun yi kira da a kauracewa shafin Twitter

Jaruman fina-finai na Hollywood da masu fafitika sun yi kira don a kauracewa shafin sada zumunta na Twitter, bayan da kamfanin Twitter ya dakatar da Rose McGowan, wata jarumar fim wanda ta zargi Harvey Weinstein wani mai shirya fina-finai da yi mata fiyade. Shafin na Twitter ya ce ta karya dokokinsu a cikin wadansu sakonni […]

Sanatocin Amurka sun soki Twitter

Sanatocin Amurka sun soki Twitter

An soki kamfanin shafin Twitter saboda ‘yar takaitacciyar bayyana wadda ba ta wadatar ba, da wakilansa suka yi a gaban kwamitin da ke binciken katsa-landan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a shekarar da ta gabata. An gayyaci jami’an kamfanin na Twitter da su bayyana domin su bayar da […]

Za a kara yawan haruffan sakon Twitter

Hukumar shafin sada zumunta da muhawara na Twitter ta ce tana duba yuwuwar kawo karshe takaita yawan haruffan da masu amfani da shafin ke yi na iya haruffa 140, inda za ta linka yawan biyu.

Daya daga cikin wadanda suka kirkiro shafin na Twitter kuma babban shugabansa, Jack Dorsey, ya ce, rubutun da masu amfani da shafin suke yi zai ci gaba da zama dan takaitacce, amma dai yawan haruffan zai iya linkawa biyu, zuwa haruffa 280, a sako daya nan gaba. Tuni dai aka fara wannan gwaji a tsakanin […]

Saudi Arabia: An Kama Yaron Da Ya Yi Rawar ‘Macarena’

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama wani yaro mai shekara 14 wanda aka nuna a wani bidiyo yana taka rawar wakar 'Macarena' a kan titi.

Saudi Arabia: An Kama Yaron Da Ya Yi Rawar ‘Macarena’

Bidiyon ya ja hankulan dubban mutane a Twitter. Hukumomi na yi wa yaron tambayoyi bayan an zarge shi da “nuna rashin tarbiyya” a birnin Jeddah, in ji wata sanarwa. Ba a tabbatar da ko yaron dan kasar ta Saudiyya ne ba, kuma ko hukuma za ta gurfanar da shi a kotu. A farkon wannan watan […]

Trump Ya Caccaki Masu Sukar Shi

Cikin fushi shugaba Donald Trump na Amurka ya ci gaba da amfani da hanyar sadarwan nan da ya saba amfani da ita wato Twitter, domin caccakar wadanda yake kallo a matsayin makiyansa, ciki harda daya daga cikin ‘yan majalisar zartarwarsa wato atoni janar na Amurka.

Trump Ya Caccaki Masu Sukar Shi

Matakin daya jawo suka daga shugabanin jam’iyar Republican da kuma kafofin yada labaru masu ra’ayin rikau wadanda galibi suke goyon ga shugaban Kwana daya baya shugaba Trump ya bayyana Atoni janar din a matsayin wanda baida wani karfin gwiwa a gare shi. Sakonin da shugaban yasa dandalin tweeter, ko tantama babu, suna nuni da cewa […]

An kai karar Trump kan hana wasu shiga Twitter

A shekara 30 da ta wuce an kai shugaban kasar Amurka Donald Trump kara kotu sau 4,000.

An kai karar Trump kan hana wasu shiga Twitter

Yanzu an kara kai shi kotu bayan da wasu mutum bakwai sun kai kararsa sakamakon toshe su da ya yi daga tofa albarkacin bakinsu a shafinsa na Twitter. Mr Trump yana amfani da Twitter sosai wajen yabon masoyansa da kuma mayar da martani ga masu sukarsa. Wata cibiya mai goyon bayan ‘yancin fadin albarkacin baki […]

An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen ‘yan sanda

An kai tsegumin Sarauniyar Ingila wajen ‘yan sanda

An kai rahoton Sarauniyar Ingila ga ‘Yan sandan West Yorkshire saboda rashin sanya maɗauri a cikin motar masarauta a kan hanyarta ta zuwa bikin buɗe zaman Majalisa. Wani mutum ne ya buga lambar kar-ta-kwana ta 999, inda ya tsegunta wa ‘yan sanda cewa Sarauniya ba ta sa bel ba a motar da ake tuƙa ta […]