Kwankwaso ko Ganduje: Waye sahihin jagoran APC a Kano?

Wata wasika da shugaban jami'iyyar APC na Arewa maso Yamma ya aika, wacce ke goyon bayan Abdullahi Abbas na bangaren Gwamna Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar a jihar Kano, na tayar da jijiyoyin wuya tsakanin magoya bayan Gandujiyya da Kwankwasiyya.

Kwankwaso ko Ganduje: Waye sahihin jagoran APC a Kano?

Tuni dai tsagin kwankwasiyya ya yi watsi da takardar, wacce ta nemi Abdullahi Abbas na tsagin Gandujiyya ya ci gaba da rike shugabancin jam’iyyar a Kano. Umar Haruna Doguwa na tsagin kwankwasiyya ya dage kan cewa har yanzu shi ne shugaban APC a Kano, don kuwa takardar ba umarnin uwar jam’iyyar ba ne. Kimanin wata […]

Doguwa ne shugaban APC a Kano – Bolaji Abdullahi

Doguwa ne shugaban APC a Kano – Bolaji Abdullahi

Uwar jam’iyyar APC ta ce har yanzu Alhaji Umar Haruna Doguwa ne, shugabanta a jihar Kano, sabanin wasu rahotanni da ke cewa an tube shi. Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi ya fitar ta ce kwamitin gudanarwar APC na kasa bai taba cim ma wata shawara game da tube […]

Jam’iyyar APC ta yi wa Ganduje ‘tutsu

Uwar jam'iyyar APC ta kasa a Najeriya ta shammaci gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, inda ta gayyaci mutumin da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar Rabiu Kwankwaso wurin taronta da mukaddashin shugaban kasa.

Jam’iyyar APC ta yi wa Ganduje ‘tutsu

Umar Haruna Doguwa, wanda ya je wurin taron, shi ne mutumin da ke ikirarin shugabantar jam’iyyar a jihar Kano, kuma mai goyon bayan Rabiu Kwankwaso ne. Sai dai Abdullahi Abbas, wanda ke goyon bayan Gwamna Ganduje ya sha cewa shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar a Kano. Lamarin dai ya sha jawo ce-ce-ku-ce a jihar, musamman […]