Nigeria Ce Ta Daya a Yaran Da Basa Zuwa Makaranta — UNICEF

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya ce kasashen Afrika su ne suka fi fama da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a duniya.

Nigeria Ce Ta Daya a Yaran Da Basa Zuwa Makaranta — UNICEF

Asusun ya ce, Najeriya kuma, ita ce ta fi yaran da ba sa zuwa makarantar a tsakanin kasashem duniya gaba daya. Wata kididdiga da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ta nuna cewa, kashi 46 cikin 100 na yara a Najeriya, ba sa zuwa makarantar gaba da firamare wato sakandire, wanda wannan adadin shi ne kusan […]

Ana Cin Zarafin Yara Shida Cikin 10 a Najeriya – UNICEF

An gudanar da taro tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyoyin masu fafutukar kare hakkin yara daga kasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki akan batun cin zarafin yara da a halin yanzu ya ke nema ya zama ruwan dare a Najeriyar.

Ana Cin Zarafin Yara Shida Cikin 10 a Najeriya – UNICEF

Wani bincike da Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi, ya gano cewa ana cin zarafin kananan yara shida cikin 10 a Najeriya. Binciken har ila yau ya nuna cewa ana kuma muzgunawa kashi 50 cikin 100 na kananan yara a kasar. Hakan ya sa masu ruwa da tsaki suka ga […]

‘Nigeria na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa’

‘Nigeria na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa’

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef, ya ce Najeriya na yin asarar $ 21bn saboda rashin shayar da nonon uwa. Shugaban Asusun a Najeriya, Anthony Lake, ne ya bayyyana haka a wurin taro kan ‘makon shayar da nonon uwa’ a Abuja, babban birnin kasar. A cewarsa, kudin da mata ke kashewa […]

Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta gargadi jama'a game da sabon salon da kungiyar Boko Haram ta bullo da shi wajen kai hare-haren kunar bakin wake kan gine-ginen gwamnati.

Boko Haram ta bullo da sabon salon harin kunar bakin wake

Mai magana da yawun Rundunar ‘yan sandan jihar, Victor Isuku ya shaida wa BBC cewa kananan yaran na kiwo ne a wani daji lokacin da ‘yan Boko Haram din suka daura musu damarar bama-baman tare da gargadinsu kada su kwance har sai sun isa gida. Ya kuma kara da cewa, ”An daura wa Gambo Bukar […]