Babu Ja Da Baya a Yaki Da Boko Haram – Kungiyar Maharba

Hadakar kungiyar maharba masu aikin sa kai da yan kato da gora a jihar Adamawa, sunyi ikirarin cewa zasu ci gaba da taimakawa sojoji a yaki da Boko Haram muddin za’a ci gaba da tallafa musu.

Babu Ja Da Baya a Yaki Da Boko Haram – Kungiyar Maharba

Kamar yadda alkalumma ke nunawa, yan sakai na maharba da kuma kato da gora da dama ne suka rasa rayukansu a yaki da Boko Haram, na baya bayan nan ma shine rashin da suka yi na wani fitaccen kwamandan Maharba Bukar Jimeta da akan yiwa kirari da kwamandan mutuwa. To sai dai kuma duk da […]