‘Amurka Bata Yi Mana Adalci Ba’

Gwamnatin Chadi ta bayyana mamaki kan yadda Amurka ta sanya kasar cikin jerin sunayen kasashen da aka hana baki zuwa Amurka, a sabuwar dokar shugaba Donald Trump.

‘Amurka Bata Yi Mana Adalci Ba’

Madeleine Alingue, mai Magana da yawun gwamnatin Chadi, tace matakin yaci karo da kokarin Chadi na yaki da ta’addanci musamman a yankin Afirka ta Yamma da kuma duniya baki daya. Gwamnatin Chadi ta bukaci shugaba Donald Trump da ya sake nazari kan matakin wanda tace ya shafi kimar Chadi da kuma dangantakar kasashen biyu. Karkashin […]

America Ta Hana ‘Yan Chadi Shiga Kasarta

Shugaba Donald Trump na sanya sabon tarnakin shiga Amurka a kan kasa takwas ciki har da a karon farko Chadi da Koriya Ta Arewa da Venezuela.

America Ta Hana ‘Yan Chadi Shiga Kasarta

Haramcin ya biyo bayan bitar harkokin tsaro da kuma nasarar da umarninsa na ainihi wanda wa’adinsa zai kare ya cim ma. Shugaba Trump ya ce yana ba da fifiko wajen mayar da Amurka, kasa mai aminci. Tasirin dokokin dai ya sha bamban daga wannan kasa zuwa waccan, inda suke haramta wa ‘yan Syria da Koriya […]

Venezuela ta daura damarar kare iyakokinta

Venezuela ta daura damarar kare iyakokinta

Gwamnatin Venezuela ta ce dakarunta dubu 200 da kuma fararen hula dubu 700 sun bi sahun atisayen soji na ranar farko da aka yi. An shirya atisayin ne bayan Amurka ta sanar da sanya takunkumin tattalin arziki a kan gwamnatin shugaba Maduro. Amurka dai na zargin Mr Maduro da yin mulkin kama karya. Shugaba Maduro […]

A siyasan ce za a magance matsalar Venezuela

Shugaban kasar Argentina Mauricio Macri ya sheidawa mataimakin shugaban Amurka Mike Pence cewar basa goyan bayan kai hari Venezuela domin magance rikicin siyasar kasar.

A siyasan ce za a magance matsalar Venezuela

Mauricio Macri ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da Pence wanda ke ziyarar wasu kasashen dake yankin, shugaba Macri yace ta hanyar siyasa ne kawai za’a magance rikicin na Venezuela. Argentina itace kasa ta baya bayan nan da ta fito karara ta bayyana adawar ta da yunkurin na shugaba Donald Trump na […]

Amurka Tana Tunanin Ko Ta Dauki Matakin Soja Kan Venezuela

Shugaba Trump ne bayyanawa manema labarai haka a gidansa dake jahar New Jersey ranar jumma'a.

Amurka Tana Tunanin Ko Ta Dauki Matakin Soja Kan Venezuela

Ahalinda ake ciki kuma, shugaban na Amurka Donald Trump, yace matakin soja yana daga cikin zabi da Amurka take dubawa kan kasar Venezuela, ya bayyana hali da ake ciki a kasar a zaman “mai hadari sosai.” Trump wand a ya bayyana haka yayinda yake magana da manema labarai a gidansa dake New Jersey, ya kara […]

Amurka ta saka wa jami’an Venezuela 13 takunkumi

Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya yi fatali da takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wasu manyan 'yan siyasa da jami'an sojin kasarsa goma sha uku.

Amurka ta saka wa jami’an Venezuela 13 takunkumi

Amurka dai ta ce ta dauki matakin domin nuna wa Mr. Maduro cewa da gaske take a barazanar ta yi na kakaba wa Venezuela takunkumi karya tattalin arziki cikin sauri idan ya ci gaba da shirinsa na gudanar da wata kuri’ar da aka shirya yi ranar Lahadi mai zuwa domin kafa wata sabuwar majalisar dokoki. […]

An lakadawa ‘yan majalisar Venezuela duka

An lakadawa ‘yan majalisar Venezuela duka

Masu goyon bayan gwamnatin Venezuela sun kutsa kai cikin majalisar dokokin kasar inda suka yi wa ‘yan majalisar da ‘yan jarida duka. Ganau sun ce lamarin ya faru ne bayan ‘yan majalisar sun gama kada kuri’a kan bikin kewayowar ranar samun ‘yancin kan kasar. Masu kutsen sun shiga majalisar dauke da sanduna sannan suka tashi […]

Jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan kotun kolin Venezuela

Jirgi mai saukar ungulu ya kai hari kan kotun kolin Venezuela

Wani jirgi mai saukar ungulu ya jefa bam a ginin kotun kolin Venezuela, a wani mataki da shugaba Nicolas Maduro ya kira fa aikin ta’addanci. ‘Yan sanda sun ce wani jami’insu ne ya dauki jirgin helikofta, kana ya jefa gurneti ta sama kan kotun kolin kasar. Hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta, sun […]