Ambaliyar ruwa ta tsayar da al’amura a Lagos

Al'amura sun tsaya cak, yayin da mutane suka kasance a gida a wasu sassan birnin Legas da ke kudancin Najeriya, bayan wani ruwansa da aka kwashe kwanaki ana yi ya haddasa ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwa ta tsayar da al’amura a Lagos

Mazauna unguwannin Lekki da Victoria Island sun wari gari ranar Asabar da ambaliyar ruwa bayan kwashe kwana biyar a ruwa, kamar yadda wata wadda take zaune a Legas ta shaida wa BBC. “Yau kwana biyar ke nan ana ruwa babu dauke wa a unguwar Lekki. Ko ‘ya’yanmu ma a cikin ruwa suke zuwa makaranta cikinsa […]