Macron Ya Mara Baya Ga Masu Kyamar Wariya A Amurka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayansa ga masu kyamar wariyar launin fata na kasar Amurka. Shugaban cikin wani sako ta shafin Twitter daya wallafa a yau karara ya nuna goyon bayansa ga masu akidar yaki da wariyar launin fatar.

Macron Ya Mara Baya Ga Masu Kyamar Wariya A Amurka

Cikin sakon da shugaban na Faransa Emmnuel Macron ya aike ya nesanta kansa  daga mara baya ga masu akidar kyamar launin fata, lamarin da kuma yazo dai-dai da bukatar da ake da ita ga mutane musamman shugabanni. Wannan sako dai bai fito fili ya kushe Shugaban Amurkan Donald Trump ba, wanda ke ci gaba da […]

Trump na fuskantar bore kan rikicin Charlottesville

Shugaban Amurka Donald Trump na fuskantar bore tun bayan furta wasu kalamai kan rikicin kabilancin daya faru a Charlottesville, al’amarin da yanzu haka ke ci gaba da sanyaya guiwar magoya bayansa, har ta kai ga murabus din wani babban jigo a tafiyar shugaban.

Trump na fuskantar bore kan rikicin Charlottesville

Lamarin dai ya buda sabon babi a tafiyar mulkin Shugaba Trump tun bayan fara aikinsa sama da kwanaki dari biyu. Kalaman na Trump dai na zargin bangarorin 2 da alhakin tayar da tarzomar wadda ta girgiza dan karamin garin na Charlottesville da ke Jihar Virginia, tare da sanadin mutuwar wata mace guda cikin masu zanga-zangar […]

Harin Charlottesville “Ya Shiga Layin Ta’addanci”

Rikicin da ya barke a yankin Charlottesville wanda ya yi sanadiyar mutum guda a jihar Virginia da ke Amurka, na ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce bayan da masu nuna fifikon fatar fata da masu adawa da su suka yi arangama a karshen makon da ya gabata.

Harin Charlottesville “Ya Shiga Layin Ta’addanci”

Mai bai wa shugaba Donald Trump shawara kan harkar tsaro ya ce mummunan tashin hankalin nan da ya auku a wurin gangamin masu da’awar fifita farar fata a Charlottesville, jihar Virginia, ya cimma abin da za a kira “ta’addanci.” A wata hira da gidan talabijin na ABC, H.R. McMaster ya bayyana abkawa da mota da […]

Ma’aikatar Shari’ar Amurka Na Binciken Mummunar Zanga-zangar Fifita Jinsin Turawa

Biyo bayan baiwa hammata iska da aka yi a taron gangamin turawa jar fata masu fifita jinsin turawa da kuma ‘yan zanga zangar da suka fito yin adawa da wannan gangamin a Jihar Virginia, an fara gudanar da bincike kan wani mai mota da ya kashe wata mata.

Ma’aikatar Shari’ar Amurka Na Binciken Mummunar Zanga-zangar Fifita Jinsin Turawa

Ma’aikatar shari’a ta tarayya a nan Amurka ta fara binciken keta hakkin bil Adama dangane da wata motar da aka tuka cikin mutane har ta kashe mutum guda a wajen wata zanga zangar nuna kin jinin gangamin da Turawa ‘yan wariyar launin fata suka shirya a garin Charlottesville dake Jihar Virginia. Atoni-janar na tarayya, Jeff […]