Nijar: Sama da Dabbobi 16,000 Sun Salwanta a Ambaliyar Ruwa

Ambaliyar ruwa a Nijar ta raba dubban mutane da gidajensu

Nijar: Sama da Dabbobi 16,000 Sun Salwanta a Ambaliyar Ruwa

Ofishin bada agajin jinkai na majalisar dinkin duniya OCHA, ya ce akalla mutane 54 ne suka rasa rayukansu, sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan da aka samu a Jamhuriyar Nijar, yayinda sama da mutane 200,000 suka rasa matsugunnasu. Ofishin majalisar dinkin duniyar ya kuma ce, mafi akasarin hasarar rayukan ya auku ne birnin Yamai, kuma a birnin […]

An Bukaci Mutane Su Kaucewa Gidajensu a Yamai Saboda Ambaliya

An Bukaci Mutane Su Kaucewa Gidajensu a Yamai Saboda Ambaliya

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun bukaci dubban mazauna yankin birnin Yammai da ke fuskantar barazanar ambaliyar ruwa su kauracewa gidajensu sakamakon ruwan saman da ake ci gaba da tafkawa a birnin. Gwamnan Yamai Soumana Ali Zataoua ya shaidawa al’ummar Yankunan da ke fuskantar barazanar ta kafar talabijin da su gaggauta ficewa daga gidajensu. A karshen mako […]

Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Jama'a daga ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo daga jinya ya kuma koma aiki, inda suke bayyana abinda suka fi so shugaban ya fi mayar da hankali a kai.

Abinda ‘Yan Najeriya Ke So Buhari Ya Fara Tunkara

Bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da jawabinsa ga ‘yan kasar mutane da dama suke ta bayyana ra’ayinsu kan abinda ya kamata ya fuskanta. A irin muhawarorin da ake ta yi, wasu sun bayyana ra’ayinsu kan abubuwan da shugaban ya kamata ya fuskanta da suka hada da tunkarar matsalar tsaro da kuma yajin […]